Kotu ta yanke hukuncin kwace kadarorin kamfanin P&ID

Kotu ta yanke hukuncin kwace kadarorin kamfanin P&ID

- Bayan amsa laifi 11 da hukumar yaki da rashawa ta EFCC ke zargin kamfanin P&ID da shi

- Lauyan EFCC ya roki kotun da ta amshe kadarorin kamfanin kamar yadda doka ta tanadar

- Alkalin babban kotun tarayya, ya yanke hukuncin karbe kadarorin kamfanin P&ID a matsayin hukuncin laifukan

Bayan amsa laifi da daraktocin P&ID da suka yi a gaban babban kotun Abuja, kotun ta yanke hukuncin kwace kadarorin kamfanin tare da mikasu ga gwamnatin Najeriya.

Kotun ta yanke hukuncin a ranar Alhamis bayan da kamfaninya masa laifuka 11 da hukumar EFCC ke zarginsa da su.

Wadanda ake zargin, Muhammad Kuchazi da Adamu Usman, wadanda sune daraktocin Kamfanin a Najeriya.

Bayan bayanan da hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta tayi, Usman ya amsa laifuka 11 da aka jero masa in da Kuchazi an kamasa da laifuka goman farko ne.

KU KARANTA: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabuwar mukaddashin shugabar ma'aikatan tarayya, Yemi-Esan

A shari'ance abubuwan da ake zarginsu sun hada da almundahanar kudade, yin amfani da ofishinsu ba yadda ya dace ba da kuma zagon ga tattalin arziki.

Bayan sun amsa laifukansu, mai shari'a ya ce ya kiyaye amsa laifukansu da suka yi tare da shaidu, sai ya yanke musu hukunci bisa ga laifukansu.

Lauyan EFCC, Bala Sanga yace "A inda masana'antar hadin guiwa ka sameta da laifi, kotu zata iya bada umarnin kwace kadarorinta."

Daga bisani, mai shari'a Edward Ekwo ya ce hukuncinsu na kunshe ne a dokokin damfara da almundahanar kudi.

"A don haka ne muka yanke hukuncin karbe kadarorin kamfanin Process and industrial Development Company don mikasu ga gwamnatin tarayyar Najeriya," in ji mai shari'ar.

"An umarci wanda aka kama da laifi na biyu da ya tattaro dukiyarsa da kadarorinsa tare da mikasu ga gwamnatin tarayyar Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel