Da duminsa: Buhari zai tafi Amurka karshen makon nan - Fadar shugaban kasa

Da duminsa: Buhari zai tafi Amurka karshen makon nan - Fadar shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari zai sake shillawa kasar Amurka a karshen makon nan domin halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya a birnin New York.

Wannan ya biyo bayan tawagar da shugaba Buhari ya tura wakilcin Najeriya a bikin rantsar da sabon shugaban taron gangamin wanda ya kasace dan Najeriya, Farfesa Bande Tijjani.

Fadar shugaban kasa ta alanta hakan ne da safen nan inda tace:

"Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi New York, kasar Amurka ranar Lahadi domin halartar taron gangamin majalisar dinkin duniya karo na 74 da aka fara ranar Talata, 17 ga watan Satumba, 2019."

Taron gangamin wannan shekarar ta musamman ce saboda dan Najeriya ke shugabantan taron gangamin."

Za ku tuna cewa a ranar 4 ga Yunin 2019, an zabi wakilin Najeriya zuwa majalisar dinkin duniya, Farfesa Tijjani Muhammad Bande, matsayin shugaban taron gangamin majalisar ta 74."

Wannan shine karo na biyu a tarihi da dan Najeriya zai rike matsayin bayan Manjo Janar Joseph Nanven Garba a shekarar 1989."

Asali: Legit.ng

Online view pixel