Sanwo-Olu ya yi wa 'yan Najeriya da suka dawo daga kasar Afirka ta kudu kyauta

Sanwo-Olu ya yi wa 'yan Najeriya da suka dawo daga kasar Afirka ta kudu kyauta

- Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya yi wa wadanda 'yan Najeriya da suka dawo daga kasar Afirka ta kudu kyauta

- Ya kuma yi alkawarin zarcewa dasu wajen koyon sana'o'i na jihar Legas din don koyon sana'a

- Mai kamfanin Air Peace ya jinjinawa matuka jirgin kamfanin sakamakon kin karbar alawus dinsu saboda sunce duk aikin kishin kasa ne

Kowanne mutum a cikin kashi na biyun dawowa daga kasar Afirka ta kudu ya samu kyautar N20,000 daga gwamnatin jihar Legas.

Mutanen sun iso ne sati daya bayan wasu 187 sun dawo daga kasar Afrika ta kudun sakamakon harin da 'yan kasar ke kaiwa bakin haure.

Mutanen cike da farinciki sun sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke jihar Legas da karfe 7:21 a jirgin kamfanin Air Peace mai lambar rijista 5N-BWI.

Shugabar 'yan Najeriya mazauna kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa ce ta karbesu tare da shugaban kamfanin Air Peace, Allen Onyema.

A tare dasu akwai Jermaine Sanwo-Olu, mai bada shawara ta musamman ga gwamnan jihar Legas akan 'yan Najeriya mazauna kasashen waje.

KU KARANTA: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabuwar mukaddashin shugabar ma'aikatan tarayya, Yemi-Esan

Jermaine Sanwo-Olu ta mika ihsanin ga wadanda su ka dawo din a madadin gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.

Sanwo-Olu ya ce za a kwashe wadanda su ka dawo din zuwa wajen koyon sana'a na gwamnatin jihar Legas din don koya musu sana'o'i daban-daban.

Dabiri-Erewa ta sanar da manema labarai cewa za a bayanan wadanda suka dawo din don cika burin gwamnatin tarayya na hada kansu.

Ta ce bayan kyautatawar kudu da aka baiwa wadanda suka dawo din, akwai kuma kungiyar masana kiwon lafiya don su bada taimako ga marasa lafiyan cikinsu.

Dabiri-Erewa ta kara da cewa wakilan Najeriya da ke kasar Afirka ta kudun na kokarin ganin an shawo kan matsalar tsaiko da ake samu wajen kwaso 'yan Najeriyar.

A bangarensa, Onyema ya sanar da manema labarai cewa akwai 'yan Najeriya da suka makale a kasar Afirka ta kudun suka kasa dawowa sakamakon rashin kudi da takardun dawowa.

Ya ce: "Kamfanin Air Peace na kwaso 'yan Najeriya ne kyauta domin nuna goyon baya ga gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma da zuciya daya."

"Kamfanin jiragen saman na bukatar gwamnatin tayi kokarinta wajen kwaso 'yan Najeriya cikin lumana. Bama bukatar kudi don munsan a karshe kudin kwaso su zai kai naira miliyan 300."

"Muna farincikin sanar muku cewa ko matukan jiragen mu sunki karbar alawus dinsu saboda sunce aikin kishin kasa ne,"

Ya yi jinjina ga gwamnatin Najeriya akan hanyar da ta bi wajen ganin an kwaso 'yan Najeriyar ba tare da hargitsi ko tashin hankula ba da kasar Afirka ta kudun. Ya kara da yin kira ga 'yan Najeriya masu hali, da su taimakawa wadanda suka dawo din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel