Kuma dai: Kotun zabe ta tsige wani dan majalisa na APC

Kuma dai: Kotun zabe ta tsige wani dan majalisa na APC

Kotun sauraron kararrakin zabe na jihar Kwara ta yanke hukunci inda ta soke zaben da ya bayyana Hon. Hassan Elewu a matsayin mamba mai wakiltan Ilotin ta kudu a majalisar dokokin jihar.

Kotun zaben a hukuncinta ta kuma bukaci a sake sabon zabe a yankin kudancin Ilorin cikin watanni uku.

Dan takaran Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 9 ga watan Maris, Jimoh Agboola ya kalubalanci zaben dan takaran APC kuma dan majalisa, Elewu akan zargin rashin cancantar tsayawa takara a zaben.

A karan mai dauke da lamba KW/EPT/HA1/2019, Agboola da jam’iyyarsa ta PDP ta hannun lauyoyinsu, Abdulwahab Bamidele da A.A. Ibrahim sun bukaci kotu tayi hukunci akan zaben Kudancin Illorin akan hujjar cewa dan takarar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben bai cancanci shiga zaben ba.

A hukucin kotun zaben wanda Justis Mariya M. Ismaila ta karanto, an magance lamarin ikon sauraron kara kan wadanda ake kara, Sulaiman Shehu Abdulsalam, APC da kuma INEC.

Kotun zaben, a matsayarta kan hurumin sauraron lamarin, ta bayyana cewa tana da ikon sauraron kara sannan cewa sashi na 138 (1) (a-e) na dokar zaben 2010 ta bata damar yin hakan.

Akan ingancin karan, Justis Mariya Ismaila ta warware almarin akan Agbola da PDP kan cewa sun gaza tabbatar da zarginsu na gabatar da takardun bogi da rantsuwar karya da suka yi akan wanda ake kara na farko.

Akan tambayan wanda ya kasance ainahin dan takarar APC a zaben tsakanin Elewu da Shehu, kotun zaben ta bayyana cewa sunan Shehu ne ke kunshe a sakamakon zaben da INEC ta kaddamar sannan kuma akwai wani hasashen kotu dake nuna cewa Sulaiman Shehu Abdulsalam ne dan takarar da jam'iyyar (APC) ta gabatar.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Najeriya ta karyata ikirarin cewa Maiduguri na karkashin hari

Duk da haka, kotun zabe ta ci gaba da gano cewa tunda dukkanin wadanda ake kara sun shaida cewa Elewu ne dan takarar APC, sannan hasashen kotu ya nuna cewa Sulaiman Shehu Abdulsalam ne dan takarar APC lamarin ya zama sokakke.

A cikin'haka, kotun zaben ta soke zaben da aka gudanar a yankin Ilorin ta kudu, sannan ta umurci hukumar INEC da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta bayar a zaben, sannan kuma tayi umurnin gudanar da sabon zabe wanda kotun tace ya zama dole ya gudana cikin watanni uku.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel