Rundunar sojin Najeriya ta karyata ikirarin cewa Maiduguri na karkashin hari

Rundunar sojin Najeriya ta karyata ikirarin cewa Maiduguri na karkashin hari

Rundunar sojin Najeriya ta karyata rahotannin cewa Maiduguri, babban birnin jihar Borno na a karkashin hari. A wani jawabi da ta saki a safiyar yau Alhamis, 19 ga watan Satumba tace a yanzu haka Maiduguri na cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Karanta jawabin a kasa:

"Bayanai da ke yawo a kafofin sadarwa sun bayyana cewa wasu makiran mutane na hasashe da yada jita-jitan cewa yan ta’adda na shirin kai munanan hare-hare akan wasu yankunan jama’a da manyan wurare a garin Maiduguri da yankunan da ke makwabtaka da ita domin haddasa tashin hankali a zukatan bayin Allah.

"Hedkwatan Operation Lafiya Dole ta ba jama’a tabbacin cewa an dauki matakan da suka kamata domin dakile mugun nufin yan ta’addan.

"Hakazalika, dakarun rundunar, sun jajirce domin tabbatar da dakile zirga-zirga da ayyukan yan ta’addan. Dakarun sun kuma dauki matakai tare da manufar manyan sansani domin domin halaka yan bindiga a duk inda suka gan su.

"Don haka, ana bukatar jama’a da su yi watsi da jita-jitan mummunan hari a Maiduguri da kewayenta. Wasu makirai da sauran masu hada kai da miyagu ne ke yada jita-jitan domin haddasa tsoro da tashin hankali a zukatan mutane domin dakile kokarin sojoji da sauran hukumomi tsaro da ke kokarin kawo karshen annobar.

KU KARANTA KUMA: Babu wata baraka da ta kunno kai a fadar Shugaban kasa – Adesina yayi martani akan ikirarin mayar da Osinbajo saniyar ware

"Ana kira ga jama’a da su yi watsi da zargin hare-hare a garin Maiduguri da kewaye sannan su tafi harkokin gabansu ba tare da tsoro ko fargaba ba.

"Ana kuma shawarta jama’a da su zuba idanu sosai sannan su kai rahoton duk wani sintiri da basu aminta dashi ba musamman a waje taron jama’a amar kasuwanni, makarantu, masallatai, cocina da kuma wajen bukukuwa."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel