Tarar $9.8bn: Kotun Najeriya ta samu direktocin kamfanin P&ID da aikata manyan laifuka

Tarar $9.8bn: Kotun Najeriya ta samu direktocin kamfanin P&ID da aikata manyan laifuka

Kamfanin 'Process and Industrial Development Ltd' a ranar Talata ya amsa laifinsa kan tuhumar da Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ke masa na aikata laifuka 11 a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.

EFCC ta gurfanar da wakilan kamfanin bisa zarginsu da aikata damfara da kin biyan haraji kan wata kwangila mai alaka da hukuncin da kotun kasar Burtaniya ta yanke a baya-bayan nan na bawa kamfanin izinin kwace kadarorin Najeriya da kudinsu ya kai dala biliyan 9.6.

Hukumar EFCC ta gurfanar da P&ID Ltd da ke Virrgin Island da reshen ta na Najeriya P&ID Nigeria Ltd kan laifuka 11 masu alaka da damfara da kin biyan haraji kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Buhari na bawa 'yan ta'adda cin hanci amma tana cin zarafin 'yan kasa na gari - Falana

Direktan kasuwanci na P&ID Virrgin Island, Mohammad Kuchazi ne ya wakilci kamfanin a kotu yayin da Adamu Usman wanda lauya ne ya wakilci P&ID Nigeria Limited

Wakilan biyu duk sun amince da laifuka 11 da mai shari'a Inyang Ekwo ya karanto musu a ranar Alhamis.

Lauyan Kuchazi, Dandison Akurunwua ne ya wakilce shi a kotun yayin da Usman ya wakilci kansa.

Laifukan da aka tuhume kamfanin da aikatawa sun hada da karyar cewa sun saya fili daga hannun gwamnatin jihar Cross Rivers a shekarar 2010 domin samar da iskar gas wadda hakan ne ya yi sanadiyar tarar dalla miliyan 9.6bn da wata kotun kasar Ingila da saka wa Najeriya.

Bayan amsa laifin na su, kotu ta umurci kamfanin na P&ID ta mika dukkan kadarorinsa ga gwamnatin tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel