Shari'ar Ganduje da Abba: PDP ta gaza gabatar da sahihan hujjoji - Lauyan INEC

Shari'ar Ganduje da Abba: PDP ta gaza gabatar da sahihan hujjoji - Lauyan INEC

Kotun zaben gwamnan jihar Kano ta kammala sauraron muhawaran lauyoyin jam'iyyar PDP da dan takararta, Abba Kabir Yusuf, da na jam'iyyar APC da dan takararta, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Kwamitin Alkalan karkashin jagorancin, Halima S Muhammad, ta ce za'a alanta ranar yanke hukunci idan kotu ta shirya.

Lauyan INEC, Ahmed Raji SAN, yayin fashin baki kan al'amarin inda ya ce an baiwa jam'iyyar PDP da Abba Kabir daman bayyana sahihan takardun shaida a kotu amma yawancin takardun shaidun ba sahihai bane, saboda haka, ya bukaci kotu tayi watsi da karar.

A jawabin lauyan gwamnan, Offiong Offiong (SAN), ya ce jam'iyyar PDP ta gaza gabatar da sakamakon da ta tattara da kanta amma ta dogara kan sakamakon da hukumar INEC ta sanar, saboda haka, kotu tayi watsi da karar.

KU KARANTA: An damke wanda ya kashe kwamandan Sojoji a Jaji

A bangaren lauyan APC kuwa, Alex Izinyon SAN, ya ce jam'iyyar PDP da Abba Kabir sun yi zargin cewa an saba doka wajen soke sakamakon zaben akwatunan zabe 207 amma basu gabatar da hujjoji akai ba. Saboda haka, ya bukaci kotu tayi watsi da karar.

Amma a bangaren lauyan PDP da Abba, Kanu Agabi SAN, ya ce babbar hujjarsu itace Abba Kabir ne ya lashe zaben zagayen farko a ranar 9 ga Maris 2019.

Ya ce hukumar INEC ta ki alanta dan takarar PDP a matsayin zakaran zabe duk da cewa an tabbatar da cewa shi ne mai rinjayen kuri'u a zagayen farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel