Babu wata baraka da ta kunno kai a fadar Shugaban kasa – Adesina yayi martani akan ikirarin mayar da Osinbajo saniyar ware

Babu wata baraka da ta kunno kai a fadar Shugaban kasa – Adesina yayi martani akan ikirarin mayar da Osinbajo saniyar ware

Wasu yan Najeriya na ta hasashen cewa an mayar da mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo saniyar ware tun bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti na musamman da za su dunga bashi shawara a kan tattalin arziki wato EAC, domin su maye gurbin majalisar tattalin arziki wacce aka fi sani da EMT wanda aka kafa a lokacin mukinsa na farko.

Yayinda Osinbajo ya jagoranci majalisar EMT, sabon kwamitin EAC da aka kafa zai dunga kai rahoto kai tsaye ga shugaba Buhari ne.

Amma hadimin Shugaban kasa na musamman a kafofin watsa labarai, Femi Adesina, wanda ya kasance bako a shirin gidan talbijin din Channels TV na Politics Today ya yi watsi da ikirarin.

Ya kuma jaddada cewa har yanzu adar Shugaban kasa guda daya ce sannan cewa akwai yawan gutsiri-tsoma da ake yi wanda yake ganin kokari ne na son haifar da baraka a tsakanin Shugaban kasa da mataimakin Shugaban kasa.

“Mataimakin Shugaban kasar ne mutum na biyu a kasar...sabon kwamitin tattalin arziki da aka kafa ma na iya zuwa ga mataimakin shugaba kasa idan bukatar hakan ta taso.

KU KARANTA KUMA: Cin mutunci ne a ce Sanatoci ba za su hau katuwar mota ba - Inji Majalisa

“Kawai dai yan Najeriya ne ke son haddasa husuma tsakanin Shugaban kasar da mataimakinsa, ta yadda suke karanta ma’aonin abubuwa da hasashe amma babu bukatar haka,” inji shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel