Kwamitin dattawan PDP sun gana da Atiku a Dubai kan zuwa kotun koli

Kwamitin dattawan PDP sun gana da Atiku a Dubai kan zuwa kotun koli

Shugabannin kwamitin amintattun jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) sun gana da dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 23 ga Febrairu, Atiku Abubakar, a Dubai, kasar UAE.

Shugaban kwamitin Sanata Walid Jibrin da sakataren, Adolphus Wabara, tare da wasu mambobi sun garzaya kasar Dubai domin tattaunawa da Atiku kan matakin da za'a dauka bayan shan kasan da sukayi a kotun zaben shugaban kasa. Daily Trust ta bada rahoto.

Sanata Jibrin ya tabbatarwa manema labarai a wayan tarho cewa lallai mambobin kwamitin sun gana da Atiku a Dubai inda suka kwashe yan kwanaki kuma suka dawo gida lafiya.

Yayinda aka tambayesa makasudin ganawar kuma dalilin zuwa kasar waje, Sanata Jibrin ya ce ba zai iya magana ba a lokaci.

Amma daga baya da aka kira wayarsa bai dauka ba kuma bai amsa tambayar a sako da tura ba.

A makon da ya gabata an kwashe akalla sa'o'i takwas ana zaman kotu kan shari'ar dake tsakanin shugaba Muhammadu Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDP, inda shugaban kwamitin Alkalan kotun, Mohammed Garba, yayi watsi da karar da PDP da Atiku suka shigar.

Alkalin ya bayyana hakan ne bayan yanke hukunci daya bayan daya kan zarge-zargen da Atiku da PDP sukayi kan nasarar shugaba Muhammadu Buhari na cewa:

1. Bai cancanci takarar zabe ba saboda bai da takardan shaidan halartan makarantan sakandare

2. An yi amfani da Sojoji da yan sanda wajen magudi zaben

3. Kuri'un da hukumar INEC ta sanar ba kai yawan wanda ke shafin yanar gizonsu

4. An ci mutuncin yan jam'iyyar PDP a jihohi 11 lokacin zabe, da sauransu

5. Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinajo, ya yi amfani da shirin Tradermoni wajen sayen kuri'u

Asali: Legit.ng

Online view pixel