Majalisar Wakilai ta gayyaci Godwin Emiefele da manyan Darektocin NDDC

Majalisar Wakilai ta gayyaci Godwin Emiefele da manyan Darektocin NDDC

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emiefele, da kuma mukaddashin shugaban hukumar NDDC mai kula da cigaban yankin Neja-Delta, za su bayyana a gaban majalisar wakilan tarayya.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, ta rahoto cewa Mai girma gwamnan CBN da Darektan na NDDC za su bayyana gaban majalisa ne domin amsa tambayoyi kan ayyukan da ake yi a yankin.

Majalisar ta koka da cewa an yi watsi da wasu kwangiloli da aka bada tun tuni a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur. Har yanzu masu alhakin hakan sun gaza karasa wannan kwangiloli.

Godwin Emiefele da Takwaran na sa wanda ke rikon kwarya a hukumar NDDC tare da Darektocinsa za su hallara gaban ‘yan majalisar wakilan ne a yau Alhamis, 19 ga Watan Satumba.

Honarabul Nicholas Ossai mai wakiltar wani yanki na jihar Delta a karkashin jam’iyyar PDP shi ne shugaban kwamitin da yake bincike game da ayyukan da ake yi a shiyyar na Neja-Delta.

KU KARANTA: Afenifere ta ce an maida Osinbajo da shi da babu duk daya a Gwamnati

Nicholas Ossai yace CBN sun ba su wasu daga cikin takardun da su ke bukata, inda yanzu su ke neman ganawa da shi kan sa gwamnan na CBN. Da karfe 12:00 ake so a ga gwamnan a majalisa.

‘Dan majalisar ya bayyana makasudin sammacin da aka yi wa CBN da manyan jami’an NDDC. Osai yace sun yi wannan ne domin taimakon mutanen Kudancin Neja-Delta da ake warewa kudi.

Binciken da mu ke yi zai nuna mana ainihin abin da ke faruwa a Neja-Delta, kuma zai sa ‘yan kwangila su koma aikin da su ka yi watsi da shi shekaru da dama da su ka wuce." Inji Hon. Osai.

Osai ya sha alwashin cewa duk ‘dan kwangilar da aka ba kudi bai yi aiki ba zai dandana kudarsa ta hanyar karbe abin da aka ba shi. Haka kuma za a biya ‘yan kwangilar da ke bi bashi kudinsu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel