Gwamnatin Buhari na bawa 'yan ta'adda cin hanci amma tana cin zarafin 'yan kasa na gari - Falana

Gwamnatin Buhari na bawa 'yan ta'adda cin hanci amma tana cin zarafin 'yan kasa na gari - Falana

Babban lauya a Najeriya, Femi Falana ya yi Allah-wadai da sumamen da jami'an tsaro suka kai a Sahara Reporters mallakar Omoyele Sowore da ofishin Kwamitin hakkin dan adam (CDHR) inda aka yi shirin yin zanga-zanga kan goyon nayan Sowore a ranar Laraba.

The Cable ta ruwaito cewa jami'an tsaron sun mamaye ofishin Sahara Reporters da CDHR da ke Legas.

Tun a watan Augusta ne jami'an 'yan sandan farar hula (DSS) suka kama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore bisa zarginsa da yunkurin tayar da hankulan al'umma da zanga-zangar juyin juya hali da ya shirya mai lakabin #RevolutionNow.

Daga bisani kotu ta bawa DSS dama tsare Sowore na kwanaki 45 domin gudanar da cikaken bincike a kansa.

DUBA WANNAN: An bayyana yadda 'yan bindiga suka bi wani basaraken arewa har gida suka kashe shi

A wani sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, lauyan Sowore, Falana ya yi tir da tsare wanda ya ke kare wa da ma wasu mutanen.

Falana ya ce, "Ya ce babban kotun tarayya ta bayar da izinin tsare Sowore na tsawon kwanaki 45 ne amma a halin yanzu DSS ta tsare shi na tsawon kwanaki 47."

"A makon da ta gabata, kotun tarayya ta ki amincewa da sabunta izinin cigaba da tsare Agba Jalingo da Ekanem Ekpo na tsawon kwanaki 14. Duk da cewa wa'adin tsare su ya kare 'yan sanda a jihar Cross Rivers sun cigaba da tsare su.

"A ranar 5 ga watan Augustan 2019 jami'an DSS sun kama Mista Abayomi Olawale suka tsare shi na tsawon kwanaki 45 ba tare da izinin kotu ba. Wadannan mutanen da wasu saura suna nan a tsare ba tare da umurnin kotu ba kuma ya kamata a sake su.

"A yayin da ya ke taya wadanda suka shirya zanga-zangar nasarar yin shirin a wani wurin daban, ba za mu amince da cin zarafi da barazana da ake yi wa 'yan kasa masu biyaya ga doka ba a karkashin gwamnatin da ke tattaunawa da 'yan ta'adda da 'yan bindiga tana basu cin hanci da kudin al'umma tare da yi musu afuwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel