Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabuwar mukaddashin shugabar ma'aikatan tarayya, Yemi-Esan

Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabuwar mukaddashin shugabar ma'aikatan tarayya, Yemi-Esan

- A jiya 18 ga watan Satumba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin Oyo-Ita da Yemi-Esan

- An bukaci Oyo-Ita da ta fuskanci zargin da hukumar yaki da rashawa ta EFCC take mata

- Yemi-Esan cikakkiyar likitar hakori ce daga jami'ar Ibadan

A ranar 18 ga watan Satumba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin Oyo-Ita da Dr Folasade Yemi-Esan a matsayin mukaddashin shugaban ma'aikatan tarayya.

Tun a shekarar 2012 ne dai Yemi-Esan ta me babbar sakatariyar ofishin kuma a ma'aikatar yada labarai da ilimi har zuwa jiya da ta samu sabon mukami.

Ga abubuwa 5 da yakamata mai karatu ya sani game da Dakta Folashade Yemi-Esan, sabuwar mukaddashin shugabar ma'aikatan tarayya.

1. Dr. Folashade Yemi-Esan ta samu digirinta na farko a fannin likitan hakori a jami'sr Ibadan a shekarar 1987.

2. Ta fara aiki a ma'aikatar lafiya ta tarayya har ta kai ga matsayin tarayya.

3. Ta kai matsayin babbar sakatariyar tarayya a 2012.

KU KARANTA: Shari'ar Abba gida-gida da Ganduje: Alkali ta ce hukuncinta ba zai zama 'inconlusive' ba

4. Ta yi aiki a matsayin babbar sakatariyar a ma'aikatar yada labarai, ma'aikatar ilimi da ma'aikatar albarkatun man fetur.

5. Ta taba hawa kujerar daraktar yada labarai a gidan gwamnati da ke Abuja daga shekarar 2012 zuwa 2014.

6. Ta yi aiki a matsayin jami'ar yada labarai ta musamman a cibiyar yada labarai, ofishin jakadancin Najeriya da ke Abidjan a kasar Cote d' Ivoire daga 1992 zuwa 1995.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel