Cin mutunci ne a ce Sanatoci ba za su hau katuwar mota ba - Inji Majalisa

Cin mutunci ne a ce Sanatoci ba za su hau katuwar mota ba - Inji Majalisa

Majalisar dattawa Najeriya ta bayyana korafin da jama’a ke yi a kan shirin ta na siyan motocin SUV na naira biliyan 5.5 ga mambobinta a matsayin cin mutunci.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Yahaya Abdullahi yace sanatocin guda 109 za su biya bashin kudin motocin a karshen shekaru hudu da za su yi kan mulki.

Yayinda yake jadadda cewar lallai su fi ministoci yin aiki, Abdullahi ya kara da cewar a matsayinsu na sanatoci sun cancanci hawa babban motar SUV.

Shugaban masu rinjayen yace: “Menene matsala a nan? Cin mutunci ne ace sanatan tarayya bai isa tuka babban mota ba a Najeriya. Cin mutunci ne. Naira biliyan 5.5 din daga kudin majalisar dokokin tarayya ne sannan kuma ana kasafinsa ne duk shekara, inda za su biya a karshen mulkinsu.

“Na kasance sakatare din-din-din a baya. Na san abunda ministoci ke samu; bama za mu iya kwatanta kanmu da ministoci ba saboda mun fi ministoci matsayi. Idan har za ku ce sanatan tarayya ba zai iya tuka katuwar mota ba a yau – toh wannan wani cin mutunci ne.

KU KARANTA KUMA: SIP: N-Power, CCT su na taimakawa Mutanen mu Inji Bala Mohammed

“Je ku fada ma mutane cewa aikin da muke yi ya fi aikin da ministoci ke yi. Nauyin da ke kaina a yau; babu miistan tarayya da ke da irin shi.”

Ya ci gaba da bayanin cewa majalisar dattawa za ta yi aiki domin ganin kananan hukuma na cin gashin kansu domin habbaka ci gaban kasa da kuma inganta tattalin arziki daga tushe, kamar yadda a yanzu suke dauke da nauyin kananan hukuma biyo bayan rushewar su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel