Matasa 'yan Jigawa 123 sun janye karar da suka shigar kan gwamnatin Legas

Matasa 'yan Jigawa 123 sun janye karar da suka shigar kan gwamnatin Legas

'Yan asalin jihar Jigawa 123 da aka kama a ranar 30 ga watan Augusta sun janye karar da suka shigar a kan gwamnatin jihar Legas na neman biyansu diyyar naira biliyan daya kan keta musu hakkinsu na dan adam.

An kama matasan ne a Moshalashi road dake Agege tare da baburansu 48 cikin wata babban mota da ke zuwa daga Jigawa.

Sun shigar da gwamnatin jihar Legas kara kan tsare su bisa ka'ida ba da keta hakkin su na 'yan adam.

Sunyi karar alkalin alkalan jihar Legas kuma kwamishinan shari'a da kwamishinan 'yan sandan jihar da kuma shugaban kungiyar tsaro ta Legas, Yinka Egbeyemi.

DUBA WANNAN: An bayyana yadda 'yan bindiga suka bi wani basaraken arewa har gida suka kashe shi

Sai dai lauyansu, Abba Hikima ya shaidawa majiyar Legit.ng a ranar Laraba cewa wadanda ya ke karewa sun janye kararsu bayan cimma wata matsaya da gwamnatin na jihar Legas.

"Abinda gwamnatin Legas tayi bai dace ba kuma sun fahimci cewa idan aka tafi kotu ba za su ci da dadi ba hakan yasa suka nemi a sassanta," kamar yadda Hikima ya fadi a ranar Laraba.

A baya, Hikima ya bayyana cewa gwamnatin jihar Legas tana tattaunawa da gwamnatin Jigawa wadda ita kuma ta ke masa matsin lamba ya janye karar amma yace ba zai janye ba sai an mayarwa matasan baburansu da motar da ta kawo su Legas.

A karar da suka shigar mai lamba FHC/L/CS/1519/19, sun bukaci kotu ta fadi karara cewa gwamnatin jihar Legas ta keta hakkinsu na izinun zuwa duk inda suke so a Najeriya karkashin sashi na 41 na kundin tsarin mulki yayin aka hana su shiga Legas ba tare da samunsu da wani abin laifi ba.

Sun bukaci kotun ta bayyana cewa an tauye musu 'yancinsu kamar yadda ya ke a karkashin sashi na 35 na kudin tsarin mulki sakamakon tsare su da hukumar tsaro ta Legas tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel