Abubakar Ibrahim ya tafi kotu domin a ba shi tikitin PDP a Jihar Kogi

Abubakar Ibrahim ya tafi kotu domin a ba shi tikitin PDP a Jihar Kogi

Rigimar da ta shiga cikin tafiyar jam’iyyar PDP ta kara cabewa bayan da daya daga cikin wadanda su ka nemi takarar gwamna a jam’iyyar, Abubakar Mohammed Ibrahim ya tafi kotu a jihar Kogi.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto jiya, 18 ga Watan Satumba, Alhaji Abubakar Mohammed Ibrahim, ya garzaya kotu inda ya nemi a tabbatar da shi a matsayin ainihin ‘dan takarar jam’iyyar.

‘Dan takarar ya bayyanawa Duniya wannan ne a lokacin da ya zanta da Manema labarai Ranar Laraba a Abuja. ‘Dan takarar ya yi jawabi ne ta bakin babban na-kusa da shi watau Shaba Ibrahim.

Ibrahim ya soki zaben da ya tabbatar da Wada Musa a matsayin ‘dan takarar PDP a jihar inda yace an yi ba daidai ba wajen tsaida shi. ‘Dan takarar ya yi watsi ne da aikin kwamitin jam’iyyarsa.

Abubakar Ibrahim ya yi mamakin yadda kuri’un da aka soke a baya, su ka koma wajen Sanata Dino Melaye. ‘Dan takarar yace don haka ba za su yarda da sakamakon zaben fitar da gwanin ba.

“A matsayin mu na masu tafiyar damukaradiyya da kuma bin doka, mun bi hanyar samun mafita da zuwa gaban Alkali, saboda yanzu maganar ta na gaban kuliya, ba za mu yi dogon bayani ba.”

Kakakin na Abubakar Ibrahim ya kara da cewa:

KU KARANTA: PDP za ta daukaka kara zuwa kotun koli a shari'ar ta da Buhari

“Abin da za mu ce shi ne, mu na rokon kotu ta tabbatar da Alhaji Abubakar Ibrahim a matsayin ainihin wanda zai rikewa jam’iyyar PDP tuta saboda kuri’un da aka soke wajen zaben tsaida gwanin.”

“Mun san da maganganun da ke yawo cewa mu na so a soke gaba daya zaben da aka yi, wannan ba gaskiya bane. Rokon mu daya ne, mun lashe zaben fitar da ‘dan takara, don haka a ba mu tikiti.”

‘Dan takarar ya tunatar da jama’a cewa ‘yan bindiga sun hargitsa duk kayan zaben da shugaban kwamitin fitar da ‘dan takarar gwamnan watau Umar Fintiri, ya yi amfani da su a Ranar 3 ga Satumba.

Mai magana da bakin ‘dan takarar, Shaba Ibrahim yake cewa bayan an kammala zabe washegari ne kwamitin ya sanar da cewa kuri’u 247 sun bace ko da cewa tazarar kuri’a 38 kurum aka samu a zaben.

Shaba Ibrahim ya ce kwamitin ya karbi kuri’u 600 a akwatin Injiniya Musa Wada, sannan aka kara masa wasu kuri’u 148 wanda wannan coge ya sa shi ya zarcewa Abubakar Ibrahim har ya samu nasara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel