SIP: N-Power, CCT su na taimakawa Mutanen mu Inji Bala Mohammed

SIP: N-Power, CCT su na taimakawa Mutanen mu Inji Bala Mohammed

Kwanakin baya ne wani gwamnan Jam’iyyar adawa a Najeriya ya fito ya na yabawa manufofi da wasu tsare-tsaren gwamnatin Tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake jagoranta.

Bala Mohammed na jihar Bauchi yake cewa ya ga tasirin tsare-tsaren SIP da gwamnatin Buhari ta kawo domin tallafawa marasa karfi inda ya tabbatar da cewa babu shakka ana ganin aikin shirin.

Mai girma gwamnnan na Bauchi ya yabawa musamman shirin N-Power wanda a cewarsa kusan ta na nan ne kurum wadanda su ka kammala makaranta su ke samun abin dogaro da zai rike su.

Gwamnan ya yi wannan bayani a lokacin da gidan Talabijin na Channels su ka taba gayyatarsa a shirinsu na Sunrise Daily. Gwamnan ya ajiye adawar siyasa a gefe guda ya yabi gwamnatin APC.

A cewar sabon gwamnan na jam’iyyar PDP, ya ji dadin wannan kokari da shugaba Buhari yake yi inda ya kuma godewa babban bankin Duniya da sauran manyan Duniya da su ke taimakon kasar.

KU KARANTA: Gwamnatin Zamfara za ta fara hada magunguna da kan ta

Bala yake cewa babban bankin Duniya ta taimaka wajen ganin ana biyan wadanda talauci ya yi wa katutu kudi N10, 000 duk wata domin ganin an yi maganin radadin talauci a fadin Najeriya.

Kamar yadda wannan bidiyo da wani Hadimin shugaban kasa, Tolu Olugunlesi ya daura a shafinsa na Tuwita ya nuna, Bala yace za a ga gyara idan har jihohi su ka hada kai da Buhari.

A kwanakin baya ma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, wanda ke mulki a a karkashin jam’iyyar PDP mai hamayya ya yabawa shugaba Buhari kan wasu ayyuka da ya ke yi a Kudu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel