Afenifere: Mu na kallon abin da ke faruwa a fadar Shugaban kasa kar

Afenifere: Mu na kallon abin da ke faruwa a fadar Shugaban kasa kar

A tsakiyar makon nan mu ka ji cewa kungiyar nan ta Afenifere ta Yarbawa, ta bayyana cewa ta na bin diddikin duk abin da ke faruwa a fadar shugaban kasa na Aso Rock ta na zura idanu.

Kungiyar ta Afenifere ta fitar da wani jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun ta, a Ranar Talata, 17 ga Watan Satumba, 2019, inda ta yi magana game da abin da ke faruwa a fadar shugaban kasa.

Wannan kungiya ta fito ta na cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo bai samu wata matsala da mai girma shugaba Muhammadu Buhari ba kamar yadda ake ta faman rade-radi.

Yinka Odumakin ya ke fadawa ‘yan jarida cewa: “Mu na kallon yadda abubuwa su ke kankama. Mu na karantar lamarin, amma ba za mu bari mu sake mu damalmala halin da ake ciki ba.”

“A yanzu, ba za mu yi gaggawar daukar matsayar cewa wannan duk shirin zaben 2023 ba. Mu na bukatar samun karin bayani domin mu fahimci ko harin siyasa ne ko kuma wuce gona da iri.”

KU KARANTA: Majalisa ta ja-kunnen wata Ministar Shugaba Buhari

Mai magana a madadin kungiyar ta Afenifere mai kare hakkin Yarbawan kasar ya kara da cewa: “Amma takaddamar da ake ta faman yi a cikin sa’o’i 48 dinnan, sun nuna akwai matsala a kasa.”

“Za mu jira mu samu bayanai masu gamsarwa, ba mu so mu fito mu ce ana gallazawa Bayarabe. Watakila ba su rasa dalilin da ya sa su ka yi haka, amma mu na sa ido kan duk abin da ke faruwa.”

Odumakin ya tike da cewa: “Babu shakka, a halin yanzu abin da ya faru shi ne, an maida ofishin mataimakin shugaban kasa maras amfani, da shi da babu duk daya, kuma bai da wani tasiri.

Kungiyar ta ce za ta fito ta bayyana matsayar ta a lokacin da ya dace. Yanzu haka dai an karbe tsarin SIP da wasu hukumomi daga karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel