Wannan abin dariya da yawa yake: Bidiyon yadda wasu 'yan sanda suka dinga bawa hammata iska a bainar jama'a

Wannan abin dariya da yawa yake: Bidiyon yadda wasu 'yan sanda suka dinga bawa hammata iska a bainar jama'a

- Yayin da gwamnati da 'yan kasa suke bukatar su hada karfi da karfe wajen yaki da ta'addanci da ya yiwa kasar nan katutu

- Can aka hango wasu jami'an hukumar 'yan sanda na kasa suna dambe a tsakaninsu tamkar zasu kashe juna

- An hangi daya daga cikin 'yan sandan da kwalbar giya a hannu yayin da shi kuma dayan aka hango shi yana kaiwa dayan naushi a fuska

Wani bidiyo da yake ta yawo a kafafen sadarwa na zamani ya nuna lokacin da wasu jami'an 'yan sanda guda biyu suka dinga dambatuwa suna tumurmusa juna a cikin bainar jama'a.

A bidiyon an hango daya daga cikin 'yan sandan yana rike da kwalbar giya yayin da dayan kuma ya dinga kai masa naushi a fuska yana neman yayi masa lahani.

Yayin da har yanzu bamu samo ainahin dalilin da ya jawo wannan rikici tsakanin jami'an 'yan sandan guda biyu ba, amma har jama'a sun dauka lamarin domin kuwa yanzu haka bidiyon ya yadu a lungu da sako na kafafen sadarwa.

KU KARANTA: Hotuna: Kakakin majalisar wakilai na kasa Femi Gbajabiamila ya shiga aji a makarantar firamare ya koyar da dalibai a jihar Katsina

A yayin da gwamnati da al'umma suke bukatarsu da su fita suje su shawo kan irin abubuwa na ta'addanci da ake fama da su a fadin kasar nan, sai suka buge da baiwa hammata iska a cikin bainar jama'a.

Dama dai mutane da yawa suna ganin babu abinda jami'an 'yan sandan Najeriya suka iya sai shiririta da kuma neman hanyar da zasu samu mutane su dinga karbar hanci babu gaira babu dalili.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel