FEC: Majalisar tarayya ta yi na’am da kwangilolin Biliyan 8.2

FEC: Majalisar tarayya ta yi na’am da kwangilolin Biliyan 8.2

Majalisar zartarwa ta tarayya, FEC, ta amince da kudi Naira biliyan 8 domin gina wasu hanyoyi hudu a Najeriya. An ci ma wannan matsaya ne bayan taron mako-makon da aka yi jiya Laraba.

A Ranar 18 ga Watan Satumban 2019, Ministoci su ka yi taron FEC a fadar shugaban kasa inda aka tattauna, kuma har aka amince da a ware kudi Naira biliyan 8.2 domin wasu aikace-aikace.

Ministan yada labaran Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana matsayar da aka cin ma a wajen taron nan wannan mako. Wannan ne zama na biyu da sababbin Ministocin kasar sun ka yi.

Shugaba Buhari ya amince da wasu takardu hudu da su ka fito daga hannun Ministan ayyuka da gidajen kasar, Babatunde Fashola. Daga ciki akwai batun sake duba kudin wasu kwangiloli.

KU KARANTA: Buhari ya canza Shugaban Ma'aikatar Gwamnatin Tarayya

Za a duba kudin da aka warewa wasu ayyukan da ake yi ne domin ‘yan kwangila su cigaba da aikinsu. Daga cikin inda aka samu canji akwai wajen ginin titin Oba Nnewi Okigwe a Kudu.

Haka zalika akwai dogon titin Alace zuwa Garin Ugep da aka karawa kudi saboda canjin da aka samu na farashin kayan aiki daga lokacin da aka bada kwangilar a shekarar 2019 zuwa yanzu.

Fashola ya kuma samu amincewar canza ‘dan kwangilan da ke yin aikin gadar Chachangi wanda ta hada Takum da Wukari a Taraba. Za kuma a taba gadar Garin Katsina ayi mata kwaskwarima.

An samu karin kudin da ya haura Naira biliyan biyu na wadannan kwangiloli da aka bada tun tuni. Titin Okigwe zai ci fiye da Biliyan 4 a yanzu, yayin da aka warewa aikin hanyar Ugep Biliyan 11.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel