An bayyana yadda 'yan bindiga suka bi wani basaraken arewa har gida suka kashe shi

An bayyana yadda 'yan bindiga suka bi wani basaraken arewa har gida suka kashe shi

Dan uwan marigayi Mohammed Bayero dagajin kauyen garin Kudunu a jihar Plateau, Mista Inusa Yaktol ya bayyana yadda wasu 'yan bindiga suka kashe basaraken.

The Punch ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun kashe basaraken ne a gidansa da ke karamar hukumar Mangu a jihar Plateau a ranar Lahadi.

Yaktol ya shaidawa kamfanin dillancin labarai NAN a ranar Laraba cewa 'yan bindigan sun ziyarci basaraken ne a gidansa misalin karfe 8 na daren ranar Lahadin.

"Marigayi Bayero yana zaune a palonsa yana kallon talabijin tare da yaransa misalin karfe 8 na dare lokacin da 'yan bindigan suka shiga gidansa.

DUBA WANNAN: Kotu ta soke zaben dan majalisar PDP, ta bayar da umarnin sake zabe

"Da shigarsu gidan sai yaransa suka shiga dakunansu domin su kyalle shi (Bayero) ya yi magana da su.

"Yaran suna tsamanin cewa 'yan bindigan baki ne kawai suka kawo masa ziyara ba tare da sanin mugun nufinsu ba.

"Bayan yaran su tafi dakinsu, makasan suka harbe shi a kirjinsa suka kashe shi nan take.

"Makasan ba su dauki komi a gidan ba kuma ba su taba kowa ba," inji shi.

Ya yi bayanin cewa makwabtan Bayero sun fito domin su duba abinda ke faruwa amma makasan suka harbi daya daga cikinsu a kafa.

NAN ta ruwaito cewa makwabcinsa da aka harba a kafa yana asibiti yana jinya.

Shugaban karamar hukumar Mangu, Mista Lawrence Danat ya yi alkawarin biyan kudin asibitin wanda 'yan bindigan suka harba a kafa.

Danat ya ce jami'an tsaro suna bin sahun wandanda suka kashe basaraken domin a hukunta su kuma hakan ya zama darasi ga sauran bata gari masu nufin aikata hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel