A karshe: Shugaba Buhari ya maye gurbin shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya

A karshe: Shugaba Buhari ya maye gurbin shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nada uwargida Dakta Folashade Yemi-Esan a matsayin mukaddashin shugabar hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya (FCSC).

A sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar a shafinta na Tuwiya a daren ranar Laraba, ta ce nadin uwargida Dakta Folashade ya fara aiki nan take, ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwar ta kara da cewa Dakta Folashade, wacce babbar sakatariya ce a ma'aikatar albarkatun man fetur, za ta maye gurbin uwargida Winifred Oyo-ita, wacce aka umarta ta tafi hutun dole maras iyaka domin bawa hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) kammala binciken da ta fara a kanta.

Kazalika, shugaba Buhari ya amince da yin karin wa'adin ritayar wasu manyan sakatarorin gwamnatin tarayya guda bakawai na tsawon shekara guda, wanda zai fara daga ranar 1 ga watan Oktoba.

Fadar shugaban kasa ta ce an kara wa manyan sakatarorin wa'adi ne domin tabbatar da ganin gwamnatin shugaba Buhari ta cimma manufofinta guda 9 da kuma bawa sabbin ministocin da aka nada damar kai bantensu.

DUBA WANNAN: Jerin al'mura 5 da Buhari ya amince da su domin murnar cika shekaru 59 da samun 'yanci

Manyan sakatarorin da aka kara wa wa'adin barin aiki su ne kamar haka:

1. Uwargida Georgina Ehuriah-Ministry, ma'aikatar harkokin cikin gida

2. Uwargida Ifeoma I. Anagbogu-Ma'aikatar harkokin mata

3. Uwargida Grace Gekpe -Ma'aikatar yada labarai da al'adu

4. Dakta Umar M. Bello-Ma'aikatar noma da raya karkara

5. Suleiman Mustapha Lawal- Ma'aikatar harkokin waje

6. Uwargida Comfort C. Ekaro - Ma'aikatar albarkatun ruwa

7. Mista Olusegun A. Adekunle- Ofishin sakatarn gwamnatin tarayya

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel