Tsohon sanatan PDP ya sauya sheka daga jam’iyyar, ya koma APC

Tsohon sanatan PDP ya sauya sheka daga jam’iyyar, ya koma APC

Wani mamba na majalisar dattawa ta shida, wanda ya wakilci yakin Bayelsa ta gabas a tsakanin 2007 da 2011 a karkashin inuwar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Sanata Nimi Barigha-Amange, a ranar Laraba, 18 ga watan Satumba, ya sanar da kudirinsa na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Ya bayyana hakan a wata wasika zuwa ga Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, wanda aka gabatar ga mukaddashin sakataren jam’iyyar na kasa, Victor Giadom a ranar Laraba.

Barigha-Amange, wanda yace yayi murabus daga tsohuwar jam’iyyarsa ta yace zai sauya sheka tare da ahlin siyasarsa, da dukkanin magoya bayansa.

Yace ya yanke shawarar sauya sheka zuwa APC sakamakon halin iko na Gwamna Seriake Dickson.

Da aka tambaye shi kan dalilin da yasa yake da tabbacin cewa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ba za ta kai laari ba, dan majalisar ya dage cewa daga cikin kananan hukumomi takwas, APC ta dauki uku yayinda PDP ke rike da biyu sannan za a yi raba-daidai a sauran kananan hukumomi uku.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin $9.bn: Majalisar wakilai za ta aika sammaci ga Malami, Sylva da sauransu

Yayinda yake maraba da mai sauya shekar, mukaddashin sakataren jam’iyyar na kasa ya bukace shi da ya mayar da hankali sannan ya hada hannu da jam’iyyar wajen samar da damokradiyya ga mutanen Bayelsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel