Yanzu-yanzu: Yan Najeriya 317 sun dawo daga kasar Afirka ta kudu

Yanzu-yanzu: Yan Najeriya 317 sun dawo daga kasar Afirka ta kudu

- Jirgin Air Peace ya sauka misalin karfe 7:21 na daren nan

- Amma an hana yan jarida isa cikin filin ajiye jirage saboda tabbata tsaro

Karo na biyu, yan Najeriya 315 sun dira babbar filin jirgin saman kasa da kasa na Murtala Mohammed dake jihar Legas da yammacin Laraba, 18 ga watan Satumba, 2019.

Yayinda suka dira misalin karfe 7:21, an garzaya da su sashen kayayyaki.

Amma an hana manema labarai isa filin ajiye jirage saboda biyayya ga dokokin tsaro.

Ma'aikatan filin jirgin saman sun nuna bacin ransu kan yadda yan jarida suka cika filin ajiye jiragen a makon da ya gabata da a sahun farko da aka dawo da mutane 187 kuma hakan ya sabawa dokoki.

KU KARANTA: Ba zai yiwu kuce PDP ta talauce ba - Ma'aikatan hedkwatan PDP sun yi ca

A jiya, ma'aikatar sufurin jirgin saman kasar Afirka ta hana jirgin Air Peace sauka a filin jirgin saman Joburg amma daga baya ta amince.

A bangare guda, Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ce gwamnatin Najeriya ba za ta kai karan kasar Afirka ta kudu majalisar dinkin duniya ba kan cin zarafin yan Najeriya a taron gangamin da zai gudana a wannan watan a birnin New York, Amurka.

Ministan ya kara da cewa ana tattaunawar diflomasiyya kan ganin yadda za'a biya yan Najeriyan da abin ya sha wasu kudade.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel