Ba zai yiwu kuce PDP ta talauce ba - Ma'aikatan hedkwatan PDP sun yi ca

Ba zai yiwu kuce PDP ta talauce ba - Ma'aikatan hedkwatan PDP sun yi ca

Shugaban kwamitin jin dadin ma'aikatan jam'iyyar Peoples Democratic Party’s (PDP), Innocent Nwankwo, ya bayyana rashin amincewar ma'aikatan jam'iyyar kan kokarin da uwar jam'iyyar ke yi na rage ma'aikata saboda rashin kudi.

Nwankwo ya ce bai zai yiwu a ce jam'iyya mai gwamnoni 19, sanatoci 40, yan majalisan wakilai 131 da yan majalisan jihohi 390 ta ce ba zata iya biyan kudin albashin dukkan ma'aikatanta ba.

Ya ce: "Babu wani arzikin jam'iyyar da ya durkushe kamar yadda suke fada saboda a yau, jam'iyyar na da gwamnoni 15, sanatoci 44, yan majalisar wakilai 131, da yan majalisar jihohi 390."

Hakalika ya karyata rahoton cewa ma'aikata 120 ke aiki a hedkwatan, ya ce maaikata 96 kacal ne.

A cewarsa: "Kudin albashin dukkan ma'aikatana wata milyan 15 ne, sabanin rahoton da ya yadu cewa milyan 65 ne."

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Yan Najeriya 317 sun dawo daga kasar Afirka ta kudu

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sanar da ma'aikatan hedkwatarta dake Abuja da kwalejin PDP cewa za ta rage yawansu.

Uwar jam'iyyar ta nada kwamiti kan aiwatar da wannan sallama amma har yanzu kwamitin bata kammala tattaunawa a kai ba.

An samu labarin cewa zancen rage ma'aikata ne babban dalilin zaman tattaunawa da ma'aikatan hedkwatar PDP da uwar jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel