Ina goyon bayan rufe iyakokin Najeriya dari bisa dari - Sarki Sanusi II

Ina goyon bayan rufe iyakokin Najeriya dari bisa dari - Sarki Sanusi II

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana gamsuwarsu a kan shawarar da gwamnatin tarayya ta dauka na rufe iyakokinta da makwabtan kasashe, tare da bayyana hakan a matsayin hanya daya tilo da Najeriya za ta tilasta yin biyayya ga dokokinta na yaki da sumogalin.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin gana wa da manema labarai a fadarsa domin jinjina wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan nada sabbin mambobin kwamitin bashi shawara a kan tattalin arziki (EAC).

Sarki Sanusi ya zargi kin biyan gwamnati haraji da wasu 'yan kasuwa masu shigo da kaya ke yi da rashin isassun matakan tsaro a iyakokin Najeriya, sannan ya kara da cewa rashin tsaro a iyakokin ya bawa barayin albarkatun man fetur saukin fita da kaya daga Najeriya.

"Idan baku manta ba, na taba yin magana a kan rufe iyakokin Najeriya da kasar Benin lokacin da shugaban kasa ya ziyarci Kano. Na dade da fahimtar cewa matukar ana son dokokin hana fasa kwauri su yi tasiri, akwai bukatar a rufe iyakokin mu.

"Wasu lokutan yana da muhimmanci a dauki matakai masu tsauri domin samun hadin kan jami'an kwastam na gida da makwabtan kasashe. Ina goyon bayan yin hakan dari bisa dari. Rufewar ta wucin gadi ce, kuma za ta kawo wa kasa cigaba," a cewar sarki Sanusi.

Da yake magana a kan sabbin mambobin EAC, sarki Sanusi ya ce shugaba Buhari ya yi abinda ya dace ta hanyar nada kwararrun masana tattalin arziki, da suka san ciki da wajen tattalin arzikin Najeriya, a cikin sabon kwamitin.

A cewarsa, shugaba Buhari ya dauki matakin da ya dace ta hanyar zabo kwararrun masana tattalin arziki masu basira domin bashi shawarwari a kan gyaran tattalin arzikin kasa a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar barazana saboda adawar kasuwanci a tsakanin wasu manyan kasashe.

Sarki Sanusi ya bayyana mambobin kwamitin a matsayin masu gogewa a bangaren tattalin arziki, tare da bayyana cewa yana da yakinin cewa zasu farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel