Hukuncin $9.bn: Majalisar wakilai za ta aika sammaci ga Malami, Sylva da sauransu

Hukuncin $9.bn: Majalisar wakilai za ta aika sammaci ga Malami, Sylva da sauransu

Majalisar wakilai na shirin aika sammaci ga ministan shari’a kuma atoni janar na tarayya, Abubakar Malami da Timpriye Sylva, karamin ministan man fetur.

Hakan na da nasaba da bukatar sake duba hukuncin tarar dala biliyan 9.6 da wata kotun kasar Birtaniya ta yanke akan gwamnatin tarayya, biyo bayan wani yarjejeniya tsakanin Najeriya da kamfanin Process and Industrial Developments (P&ID), a lokacin gwamnatin baya.

Domin sake nazarin hukuncin, majalisar wakilai a ranar Laraba, 18 ga watan Satumba, ta kafa wani kwamitin wucin gadi da suka hada da mambobi 17 karkashin jagoracin Hon. Sada Soli daga jihar Katsina, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ana so Malami da Sylva su bayar da shawarwarin kwarru akan yiwuwar kura-kurai da ke tattare da hukucin sannan kuma su samar da hanyoyin guje ma sake afkuwar hakan a nan gaba.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 3 da zan fi ba muhimmanci a matsayin Shugaban zauren UN – Bande

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bada umarni ga EFCC, NIA da Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya da su binciko kwangilar da ke tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin 'The process and industrial Developments Limited' wacce aka sa hannu a shekarar 2010.

Kwangilar mai cike da sarkakiya, itace tushen barna dala biliyan 9.6 da ake bin Najeriya wanda kotun Birtaniya ta yanke hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel