Abubuwa 3 da zan fi ba muhimmanci a matsayin Shugaban zauren UN – Bande

Abubuwa 3 da zan fi ba muhimmanci a matsayin Shugaban zauren UN – Bande

Ambasada Tijjani Mohammed Bande, sabon shugaban babban zauren majalisar dinkin duniya wacce aka fi sani da UNGA, ya bayyana cewa zai mayar da hankalinsa kacokan akan wasu muhimman abubuwa guda uku.

Bande ya bayyana wadannan bangarori uku da zai ba kula a matsayin:

1. Kawar da yunwa da talauci

2. Samar da ingantaccen ilmi

3. Jan sauran kasashe a jikin Majalisar Dinkin Duniya

Bande wanda ya kasance dan Najeriya ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi tare da manema labaran Majalisar dinkin duniyan.

Ya jaddada cewa idan idan aka samar da ilmi mai inganci, hakan zai daidaita komai da kowa. Ya danganta alakar da ke tsakanin ilmi da kuma samar da aikin yi da daidaiton al’umma da kuma sanin ‘yancin su tare da ba su wannan ‘yancin.

“Duk wanda aka hana ilmi, to a hakikanin gaskiya an tauye masa komai na rayuwa."

Da ya ke magana a kan fatara, yunwa da talauci, Bande ya ce idan har kasashe mambobin Majalisar suka bayar da goyon baya, toh lallai za a samu gagarumin ci gaba ta bangaren kawar da kuncin rayuwa a cikin milyoyin al’ummar kasashen duniya.

KU KARANTA KUMA: Wata dalibar jami’a ta kashe saurayinta akan N2,500

“Ana bukatar kowace kasa ta gabatar da bayanan duk wani kokari ko yunkuri aka yi a kasar wanda ya yi tasiri da wanda bai yi ba, domin a sake nazarin yadda za a samu hanya daya mafita.”

Ya kuma nuna irin kokarin da za a yi domin rage gibin da ake samu wajen tazarar da ake bai wa kananan yara mata a fannin samar da ilmin zamani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel