Jerin al'mura 5 da Buhari ya amince da su domin murnar cika shekaru 59 da samun 'yanci

Jerin al'mura 5 da Buhari ya amince da su domin murnar cika shekaru 59 da samun 'yanci

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da jerin wasu al'amura a matsayin shagalin murnar bikin cikar Najeriya shekaru 59 da samun 'yanci.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga Willie Bassey, darektan yada labarai a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Al'amuran shagalin bikin zasu fara ne ranar Litinin 23/09/2019 da wani taro da manema labarai a cibiyar 'yan jarida da ke birnin tarayya, Abuja.

Za a yi addu'o'i yayin Sallar Juma'a a a ranar 27/09/2019, sannan za a gabatar da lakca ta musamman a babban Masallacin kasa da ke Abuja.

Za a gudanar da wasu addu'o'in na musamman a ranar Lahadi 29/09/2019 yayin ibadar mabiya addinin Kirista a cibiyar mabiya addinin Kirista da ke Abuja.

Za a gabatar da wani taron matasa na musamman (NYEES2) a cibiyar taron kasa da kasa da ke Abuja a ranar Litinin 30/09/209.

A dai ranar ta Litinin, za a sake yin wani taron na matasa a 'Millenium Park' da ke Abuja.

Shugaban Buhari zai tattauna da manema labarai da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar Talata 01/10/2019.

Za a gabatar da lakca da kade-kade da raye-raye na musamman a fadar shugaban kasa a ranar Talatar da daddare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel