Hari a matatar man kasar Saudi: Ba mu da hannu a ciki – kasar Iran

Hari a matatar man kasar Saudi: Ba mu da hannu a ciki – kasar Iran

Ma’aikatar harkokin kasashen waje ta kasar Iran ta musanta zargin da gwamnatin kasar Saudiyya take mata na cewa tana da hannu a harin da aka kai ma matatar man kasar Saudi, inji rahoton jaridar Blue Print.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Iran ta bayyana haka ne cikin wata wasika data aika ma gwamnatin kasar Amurka ta hannun ofishin jakadancin kasar Swizterland dake Tehran, inda tace:

“Bamu da hannu cikin harin da aka kai ma kasar Saudi. Don haka idan aka aka taba mu saboda wannan, zamu dauki mataki wanda ba zai yi ma kowa kyau ba.”

KU KARANTA: Daliban makarantar Islamiyya 26 sun mutu a sanadiyyar tashin gobara

A ranar Asabar, 13 ga watan Satumba ne aka kai hari a matatar man fetir na Saudiya wanda hakan ya janyo asarar fiye da rabin man dake matatar gaba daya, wannan hari ya tayar da hankula a yankin gabasa na tsakiya.

Sai dai kungiyar mayakan yan Shia na Houthi dake kasar Yemen sun dauki alhakin kai wannan hari, tun a shekarar 2015 Houthi dake yaki da Sojojin kasar Yemen dake samun goyon bayan gwamnatin kasar Saudiyya.

Amma jim kadan bayan harin, sakataren kasar Amurka, Mike Pompeo ya zargi kasar Iran da kai wannan hari, inda Iran ta karyata shi, kuma ta ce ya yi haka ne domin su samu hujjar daukan mataki a kanta.

A yanzu haka ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Iran tace za’a yi wata ganawar sirri tsakanin yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, Muhammad Bin Salman da sakataren Amurka domin su tattauna a kan harin, tare da samar da mafita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel