Shikenan wahala ta kare: ECOWAS za ta tilasta gwamnatin Najeriya ta bude boda

Shikenan wahala ta kare: ECOWAS za ta tilasta gwamnatin Najeriya ta bude boda

- An bukaci gwamnatin Najeriya da ta bude iyakar da ta rufe a yankunan Afrika ta yamma

- 'Yan majalisar ECOWAS ne suka roki gwamnati akan ta bude bodar a ranar 16 ga watan Satumbar nan

- Honorabul Moustapha Cisse Lo ya ce rufe bodar ba shine mafita akan matsalar da ake samu ta shigo da kaya ta barauniyar hanya ba

A ranar Litinin dinnan ne 16 ga watan Satumbar nan, majalisar ECOWAS ta roki gwamnatin Najeriya da ta bude bodar da ta rufe, saboda rufewar ya kawo rashin cigaba na kasuwanci a kasashen Afrika ta Yamma.

Kakakin majalisar, Honorabul Moustapha Cisse Lo, shine yayi wannan rokon a wata sanarwar a lokacin bude wani taro na majalisar a birnin Monrovia na kasar Liberia.

Ya kara da cewa rufe bodar ya kawo matsala a bangaren kasuwancin da ake yi a kasashen Afrika, yayin da kuma ake kokarin ganin an cire duk wata hanya da za ta kawo rashin cigaba ga al'ummar yankin.

KU KARANTA: Ga irinta nan: 'Yan Najeriya guda biyu sun mutu bayan kwayar da suka hadiye a filin jirgi ta fashe a cikinsu

Haka kuma Cisse Lo, ya bukaci bukaci gwamnatin Najeriya da ta nemo mafita akan matsalar da take fama da ita ta shigo da kaya ta barauniyar hanya, ba wai rufe boda ne mafita ba, domin kuwa hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

Bayan haka kuma Cisse Lo, ya nuna cewa a shirye yake domin 'yan majalisar ECOWAS din su zo su zauna suyi magana akan kasafin kudin majalisar na shekarar 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel