Bola Tinubu ya samu lambar yabon siyasa daga kungiyar APC a kasaHabasha

Bola Tinubu ya samu lambar yabon siyasa daga kungiyar APC a kasaHabasha

Babban Jigon jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya samu kyautar damukaradiyya ta Afrika. Daily Trust ta rahoto mana wannan a Ranar Laraba 18 ga Satumba.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana dazu nan, an ba tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu wannan kyauta ne a dalilin irin kokarin da ya yi wajen ganin cigaban damukaradiyya a Najeriya.

An ba Bola Tinubu wannan kyauta ne a wajen wani taron siyasa da aka shirya a Garin Addis Ababan Habasha. Wannan shi ne karo na hudu a Duniya da aka shirya wannan babban taro.

Manyan ‘yan siyasan Nahiyar biyu, kungiyar ta APC ta karrama a babban birnin na kasar Habasha ganin irin gwgwarmyar da su ka yi wajen habaka siyasa da zamatakewa a kasashen su.

Bayan wannan lambobobin yabo da aka bada, an yi taron kwana uku inda aka tattauna kan batutuwan da ke damun kasashen Afrika wanda su ka hada da tara kudin yakin neman zabe.

KU KARANTA: Mai dakin Gwamnan Najeriya za ta dauki dawainiyar Marayun jihar ta

Kungiyar APC watau "Association of Political Consultants" hadaka ce ta manyan masana harkar siyasa a Afrika. Kehinde Bamigbetan wanda shi ne shugaban wannan kungiya ya halarci bikin.

A cewar Bamigbetan, Tinubu ya taka rawar gani wajen ganin jam’iyyarsa ta APC ta doke PDP mai rike da mulki a zaben 2015 inda ‘dan adawa Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa.

Mutum na biyu da aka karrama shi ne shugaban kasar Habasha, Abiy Ahmed Ali. APC ta yabawa kokarin Abiy musamman wajen kawo zaman lafiya a kasar sa da kuma sasanta rikicin Eretria.

Asiwaju Tinubu bai samu halartar wannan taro ba amma Alhaji Mutiu Are, wanda ya na cikin manyan jam’iyyar APC a jihar Legas ya samu halarta a madadinsa inda ya nuna farin cikinsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel