Dalilin da yasa muka mamaye ofishin CDHR da 'Sahara Reporters' - Rundunar 'yan sanda

Dalilin da yasa muka mamaye ofishin CDHR da 'Sahara Reporters' - Rundunar 'yan sanda

A ranar Laraba ne jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya suka mamaye ofishin gidan jaridar 'Sahara Reporters' da ofishin wata hukuma da ke rajin kare hakkin bil'adama (CDHR) a jihar Legas.

Jami'an rundunar 'yan sanda dauke da bindigu sun isa sakatariyar CDHR ta kasa da ofishin 'Sahara Reporters' duk a karamar hukumar Ikeja da ke jihar Legas da misalin karfe 6:00 na safe.

Jami'an 'yan sandan basu bar ofisoshin ba har zuwa yammacin ranar Laraba.

'Yan sandan sun mamaye ofisohin ne domin dakile wata zanga-zanga da aka yi niyyar gudanar wa domin neman a sako dan gwagwarmaya Omoyele Sowore daga gidan yari.

Da jaridar Premium Times ta tuntubi Bala Elkana, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, ya ce an tura 'yan sanda wuraren ne domin tabbatar da tsaro da biyayya ga doka.

"An tura su wuraren ne domin tabbatar da tsaro da kuma tabbatar da cewa ba a samu wata barazana ga zaman lafiya ba," Elkana ya fada a takaice.

DUBA WANNAN: Gyara: Buhari ya bukaci hukumar PSC ta daidaita sahun rundunar 'yan sandan Najeriya

Da wakilin jaridar ya ziyarci wurin da ofishin Sahara Reporters ya ke, ya ga motocin 'yan sanda guda biyu da jami'an 'yan sanda a kalla 10 dauke da bindigu suna muzurai.

Kazalika, a hedikwatar CDHR ta kasa akwai motocin 'yan sanda 25 da jami'an 'yan sanda a kalla 25 dauke da bindigu suna kewaya wa.

An ajiye motoci hudu a bakin kofar shiga hedikwatar, yayin da aka ajiye wasu motocin biyu a tsallaken titin da ke kallon ofishin.

A cikin watan Agusta ne jami'an tsaro na farin kaya (DSS) suka cafke Sowore tare da yin awon gaba da shi bayan ya shirya gudanar da zanga-zangar juyin juya hali a fadin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel