Baya mai goya marayu: Uwargidan gwamnan Zamfara za ta dauki nauyin karatun marayu

Baya mai goya marayu: Uwargidan gwamnan Zamfara za ta dauki nauyin karatun marayu

Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Balkisu Matawalle a ranar Laraba 18 ga watan Satumba, 2019 ta dauki alkawarin hada hannu da kungiyoyi masu zaman kansu domin bai wa marayu ilimi.

Uwargidan gwamnan ta yi wannan furucin ne a wurin taron cika shekaru biyu na kungiyar Juvenile Aid Foundation, inda ta ce za ta mayar da hankali wurin samar da ilimi ga marayu da kuma masu karamin karfi a jihar.

KU KARANTA:An haramta shan sigari a kasar Indiya

Balkisu Matawalle wadda ta samu wakilcin hadimarta mai suna Hajiya Samira Baffa ta jinjinawa kungiyar bisa namijin kokarinta na daukan nauyin ilimin marayu sittin a jihar.

“Ina taya shuwagabanni da kuma ilahirin ma’aikatan Juvenile Aid Foundation murnar cika shekaru biyu tare da samun gagarumar nasara cikin wadannan shekarun.

“Ina mai shaida maku cewa wannan shekarar ta murna ce sannan kuma murnar ta sha bamban da irin wadda kuka saba yi. Muna kokarin ganin yadda zamu hada hannu da ku domin daukan nauyin karatun marayu.

“Ina sane da cewa kungiyarku a halin yanzu tana dauke da nauyin karatun marayu sittin (60). Ko shakka babu wannan abinda da ku kayi ya cancanci a yaba maku.” Inji uwargidan gwamnan.

Hajiya Balkisu ta sake yin umarni ga shuwagabannin kungiyar da su bata a rubuce kasafin abinda za’a kashewa wasu zubin marayun domin ilimantar da su.

“Hakika na yi farin ciki da irin wannan aiki da kungiyarku ke yi. Ayyukan naku sun zo daidai da muradan Gwamna Bello Matawalle na samar da ingantaccen ilimi ga yaranmu.” Uwargidan gwamnan tayi karin haske.

https://www.vanguardngr.com/2019/09/zamfara-governors-wife-to-sponsor-orphans-education/?utm_source=dlvr.it&utm_medium=twitter

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel