Jam'iyyar APC ta ki amince da hukuncin kotun kan Sanata Adeyeye

Jam'iyyar APC ta ki amince da hukuncin kotun kan Sanata Adeyeye

Shugaban jam'iyyar APC na yankin Ekiti ta Kudi, Akin Akinbobola a ranar Laraba ya ce soke zaben shugaban kwamitin kafafen yadda labarai da hulda da jama'a na majalisar dattawa, Sanata Adedayo Adeyeye da kotun sauraron karrakin na Ado Ekiti tayi hana al'umma abinda suke so ne.

The Punch ta ruwaito cewa Akinbobola ya ce hukuncin da kotun ta yanke a makon da ya gabata na soke nasarar Adeyeye "ya daure musu kai kuma hana al'ummar mazabar Ekiti ta Kudu abinda suke so ne."

Shugaban jam'iyyar da ya yi magana a Omuo Ekiti, a yayin wani taron masu ruwa na jam'iyyar APC a yankin ya ce, "Hukuncin rashin adalci ne. Jam'iyyar APC ce ta lashe zaben ranar 23 ga watan Farbrairu a mazabar ba tare da magudi ba."

DUBA WANNAN: Kotu ta kwace kujerar dan majalisa PDP a jihar Sokoto, ta bayar da umurnin yin zaben raba gardama

Akinbobola ya ce, "Munyi mamakin hukuncin da kotun zaben ta fitar. Ba mu amince da shi ba kuma ba zai dore ba saboda al'umma ne suka zabi APC. Anyi niyyar a kwace mana nasarar mu ne kuma a jefa rashin jituwa a jam'iyyar mu."

Wani shugaban matasa na APC a Ekiti ta Gabas, Gbade Olusegun da ya ce Adeyeye na yi nasara ne ta hanyar zabe mai tsafta ya kara da cewa, "Kotun ta yanke hukuncin ta amma muna da tabbas cewa murnar da abokan hamayya ke yi gajeruwa ce. Ba zamu bari PDP ta sace nasarar da al'umma suka bawa Adeyeye ba."

Wata shugaban mata na jam'iyyar APC, Rachael Ibukun ta ce tayi imanin cewa kotun daukaka kara za tayi adalci a kan zaben inda ta ce, "Kotu ita ce gatan talaka kuma muna fatan cewa murnar da 'yan adawa ke yi gajeruwa ce."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel