An haramta shan sigari a kasar Indiya

An haramta shan sigari a kasar Indiya

Gwamnatin kasar Indiya ta hana shan tabar sigari wadda ke amfani da lantarki a kasar gaba daya saboda irin illar da ta keyiwa lafiyar jikin dan adam.

Ministan kudi na kasar Indiya, Nirmala Sitharaman ne ya bada wannan sanarwar a ranar Laraba 18 ga watan Satumba, 2019.

KU KARANTA:Amfani da cajar waya ta aro kan iya zama sanadiyar sace wayarka

Ministan ya ce: “Majalisar zartarwar gwamnatin kasar Indiya ta aminta da haramcin duk wani nau’in fataucin sigari da ya hada da shigowa ko fitar da ita daga kasar.”

Haka zalika wannan hanin bai tsaya kan sigarin kadai hadda abubuwa masu kama da ita tabar wato sigari, kamar yadda Nirmala ya fadi.

Rahotanni sun bayyana mana cewa sigarin mai amfani da lantarki ba a kasar Indiya ake sarrafa ta ba, shigo da ita ake yi kasar.

Babban sakataren ma’aikatar lafiya ta kasar Indiya, Preeti Sudan ya ce akwai tara ga duk wanda aka samu ya aikata laifin sha ko fataucin sigarin. “Wanda aka kama a karo na farko zai shekara guda a gida yari tare da tarar Rupee 100,000 wanda yake daidai da $1,404 ta Amurka.

“Idan kuma an taba kama mutum yayi gangancin barin a sake kama shi, to zai shekara uku gidan yari tare da tarar Rupee 500,000.

“A halin yanzu dai babu wani bincike a kasar nan tamu ta Indiya da ya bayyana mana hakikanin illar da shan sigarin ke haifawar a jiki, amma binciken kasar Amurka ya tabbatar mana da cewa matasan dake zukan tabar ba ta yi masu komi in ba illa ba ga lafiyar jikinsu.” Inji Sudan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel