Zaben gwamnan Kano: Kotu ta jingine hukunci

Zaben gwamnan Kano: Kotu ta jingine hukunci

Kotun zaben gwamna na jihar Kano a ranar Laraba, 18 ga watan Satumba, ta jingine hukunci akan karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta na zaben gwamna, Abba Kabir Yusuf suka shigar.

PDP da Kabir-Yusuf na kalubalantar kaddamar da Gwamna Abdullahi Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 23 ga watan Maris.

Justis Halima Shamaki, Shugaban kotun zaben bayan sauraron jam’iyyun a kan lamarin ta bayyana cewa za a sanar masu da ranar yanke hukunci.

Shamaki tayi godiya ga jam’iyyun akan goyon bayan da suka ba kotun zaben domin tayi adalci kan dukkan lamuran da ke gabanta.

Da farko, lauyan INEC, Ahmad Raji (SAN), yayinda yake gabatar da rubutaccen jawabansa na karshe, ya roki kotun zaben da ta yi watsi da karar akan rashin fa'ida.

KU KARANTA KUMA: Wasu kishiyoyi sun lakada wa mijinsu dukan tsiya bayan yayi kokarin auren mata ta uku

Raji ya bayyana cewa INEC bata yi kumbiya-kumbiya ba wajen gudanar da aikinta akan shaidun da ta gabatar a gaban kotun zaben.

Lauyan Ganduje, Offiong Offiong (SAN), da yake gabatar da rubutaccen jawabansa na karshe, shima ya roki kotrtun zaben da ta yi watsi da karar.

Ya bayyana cewaa takardun sakamakon da masu kara suka gabatar bai da fa'ida sannan cewa kotun zaben tayi watsi da lamarin.

Mista Alex Eziyon (SAN), lauyan APC ya bayyana karar PDP a matsayin mai rauni.

Eyizon ya fada ma kotun zaben cewa INEC na da ikon soke sakamakon zabe ko kaddamar da wanda yayi nasara a cibiyar tattara sakamako sannan ya bukaci kotun da tayi watsi da karar.

Adeboyega Awomolo (SAN) wanda ya yi martani a madadin lauyan masu kara ya bukaci kotun zaben da ta kaddamar da Abba Kabir-Yusuf na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Awomolo ya roki kotun zaben da tayi adalci ga dukkanin korafe-korafen da aka gabatar a gabanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel