NMCN za ta dawowa da ABU lasisin makarantar koyon jinyarta da ta kwace

NMCN za ta dawowa da ABU lasisin makarantar koyon jinyarta da ta kwace

- Babban sakataren kungiyar NMCN yace kungiyar a shirye take don dawowa da lasisin makarantar koyon jinyar jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria

- Ya ce dama rashin bin dokar kungiyar ne yasa suka kwace

- Majalisar wakilai sun saka baki kuma hukumar makarantar ta yi abinda ya dace

Babban sakataren kungiyar malaman jinya da ungozoma ta Najeriya, NMCN, Faruk Abubakar ya bayyana cewa a shirye suke don dawo da yarjewarta ga makarantar koyon aikin jinya ta jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Idan zamu tuna, a watan Mayu na wannan shekarar ne NMCN ta janye yarjewarta na ingancin makarantar koyon jinyar ta jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Janye yarjewar kungiyar ta biyo bayan zaben Hayat Gommaa, malamar jinya 'yar kasar Egypt a matsayin shugabar makarantar jinyar bayan kuma bata da rijistar kungiyar.

Abubakar, ya yi magana da Daily Post a Abuja a ranar Talata, ya bayyana cewa kungiyar ta sauko daga dokin na-kin da ta hau, bayan saka bakin majalisar wakilan Najeriya da kuma bin doka da hukumar jami'ar Ahmadu Bello ta yi.

KU KARANTA: Damuwa a fadar shugaban kasa a kan makomar mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo

Babban sakataren ya ce: "Zabar Hayat Gommaa, 'yar kasar Egypt wacce ba ta da rijistar kungiyar a matsayin shugabar makarantar jinyar har na tsawon shekaru 8 yasa muka janye yarjewarmu. Kafin nan mun turawa hukumar makarantar wasiku da dama akan illar abinda suka yi."

"Kungiyar ta bukaci hukumar jami'ar da ta turo takardun shaidar karatun matar don tantancewa da kuma tabbatar da ta kai yadda muke tsammani."

"Hakazalika, majalisar tarayya ta sa baki kuma jami'ar Ahmadu Bello a bangarenta ta zabo wanda ke da rijistar kungiyar a matsayin shugaba makarantar koyon aikin jinyar."

"A bangaren mu kuma, a shirye suke don dawo da yarjewarmu yadda za a cigaba da karatu. Wannan zai biyo baya ne in hukumar jami'ar ta turo da wasika don sanar damu cewa ta nada wanda ya cancanta."

"Sun riga sun sanar da cewa sun zabi malamin jinya mai rijistar Kungiyarmu kuma Dan Najeriya. Bamu da matsala akan hakan, amma dole ne a zabi wanda ya cancanta kuma Dan kungiyar NMCN," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel