Kotu ta soke zaben dan majalisar PDP, ta bayar da umarnin sake zabe

Kotu ta soke zaben dan majalisar PDP, ta bayar da umarnin sake zabe

Kotun sauraron karrakin zabe da ke birnin Oweri a ranar Laraba ta soke zaben dan majalisar wakilai na tarayya, Obinna Onwubuariri.

Kafin soke zabensa, Onwubuariri ne ke wakiltan mazabar Isiala Mbano/Onuimo/Okigwe na jihar Imo a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

An zabi shi a matsayin dan majalisa ne karo na farko a shekarar 2015.

A yayin yanke hukuncin da aka kwashe kimanin awa biyu, Shugaban kotun, R. Harriman ta umurci INEC ta sake sabon zabe cikn kwanaki 90 daga ranar da aka yanke hukuncin.

A cewar alkalan, wanda ta shigar da karar, Princess Miriam Onuoha na jam'iyyar APC ta gamsar da kotu da hujojji kwarara kan karar da ta shigar da na kallubalantar zaben.

DUBA WANNAN: Majalisar Kano ta roki wani muhimmin alfarma daga wurin Ganduje

Kotun ta bayar da umurnin da kwace takardan shaidan kashe zabe da aka bawa wanda akayi karar shi a gabanta ba tare da bata lokaci ba.

Harriman ta ce an saba wa dokokin zabe yayin da aka mika wa dan majalisar nasarar zaben.

Hadimin wacce ta shigar da karar, Isreal Onyema ya shaidawa manema labarai cewa mai gaidansa za ta fi murna idan kotun ta ce a mika wa jam'iyyar APC nasarar zaben na ranar 21 ga watan Fabrairu.

Onyema ya ce mai gidansa ce ta lashe zaben a kananan hukumomi uku da ke mazabar.

Wani hadimin dan majalisar da aka soke zabensa ya ce mai gidansa zai daukaka kara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel