Buhari ya sake fitar da wasu hukumomi 6 daga karkashin Ofishin Osinbajo

Buhari ya sake fitar da wasu hukumomi 6 daga karkashin Ofishin Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kara sake rasa iko da wasu hukumomin gwamnatin tarayya da ke karkashin kulawarsa, kamar yadda rahotanni suka nuna a ranar Talata.

A cewar jaridar Daily Trust, majiyarta a fadar shugaban kasa ta sanar da ita cewa an aika wa Osinbajo takarda daga ofishin shugaban kasa a kan ya nemi izinin shugaba Buhari kafin zartar da wani hukunci ko daukan mataki a kan al'amuran da ya shafi hukumomin.

Hukumomin da ke karkashin ofishin Osinbajo sun hada da hukumar bayar da agajin gagga wa ta kasa (NEMA), hukumar raya garuruwan da ke kan iyakokin kasa (BCDA), makarantar horon manyan jami'an gwamnati (NIPSS) da hukumar kula da iyakokin kasa (NBC).

Kazalika, Osinbajo ne ke jibintar al'amuran kwamitin darektocin kamfanin raba hasken wutar lantarki na yankin Niger Delta (NDPHC) da kuma kwamitin gwanjon kadarorin gwamnati (NCP).

DUBA WANNAN: Fatan da nake yi wa Najeriya - Bill Gates

Sabon umarnin na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin tafka badakala wajen gudanar da harkokin da suka shafi hukumomin. Fadar shugaban kasa ba ta bayar da wani dalili a kan yin hakan ba.

Sai dai, wani jawabi da ya fito daga ofishin Osinbajo a daren ranar Talata ya ce mtaimakin na shugaban kasa bai saba wata ka'ida ba wajen tafiyar da harkokin hukumomin.

Amma wasu rahotanni sun nuna cewa yin hakan na daga cikin manufofin shugaba Buhari na rage nauyin da ke rataye a wuyan fadar shugaban kasa, kamar yadda ya ke a cikin manufofin gwamnatinsa a zango na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel