Amfani da cajar waya ta aro kan iya zama sanadiyar sace wayarka

Amfani da cajar waya ta aro kan iya zama sanadiyar sace wayarka

Jaridar Forbes ta ruwaito cewa masana kan harkar da shafin tsaron yanar gizo sun yi gargadi ga al’umma cewa su guji yin amfani da na’urar chajin waya ta aro.

Ya riga da ya zama ruwan dare a halin yanzu, mutane ba su dauki hakan komi ba da zarar mutum ya bukaci yin cajin wayarsa zai ari caja daga hannun wani a makaranta ko kuma wurin aiki, ba tare da la’akari da abinda wannan irin aiki zai janyo ba.

KU KARANTA:Ina nan da raina ban mutu ba - Maryam Yahaya

A wurin wani taron na musamman wanda aka sabawa shirya duk shekara a Las Vegas karkashin jagorancin Charles Henderson ya yi gargadi a kan aikata irin wannan aiki.

Charles ya ce: “Ku rika lura da irin na’urar da kuke amfani da ita domin cajin wayoyinku, wannan wata hanya ce ta tsare wayoyinku.”

Bugu da kari, ya bayyana yadda ya tara gun-gun wasu masu kwarewa a fannin damfara ta yanar gizo inda suka yi kokarin dakatar da caja daga yiwa wani daban amfani matukar ba mai asalin wayar bane.

A wurin taron wani kwararre ya nuna yadda sabbin na’urorin cajin wayar ke aiki a yanzu. Da zarar an laka cajar a waya dan damfara zai samu duk wani bayani game da wayar, kuma zai iya goge duk daftarin dake cikin wayar.

Henderson ya sake jan hankali game da irin wannan ta’adi inda ya ce, bai riga da zama gama ga gari ba a halin yanzu amma akwai bukatar jama’a su lura kwarai da gaske kafin abin yazo yafi karfinsu.

Ya kuma kara da bada shawara ga jama’a na su guji yin amfani da wuraren caji na gama gari musamman a wurin da jama’a ke taruwa kamar tashar jirgin sama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel