Ga irinta nan: 'Yan Najeriya guda biyu sun mutu bayan kwayar da suka hadiye a filin jirgi ta fashe a cikinsu

Ga irinta nan: 'Yan Najeriya guda biyu sun mutu bayan kwayar da suka hadiye a filin jirgi ta fashe a cikinsu

- 'Yan Najeriya guda biyu sun rasa rayukansu bayan sun hadiye wasu kwayoyi masu tarin yawa da zasu hana a kamasu a filin jirgi

- Kwayoyin da suka hadiye din sun fashe ne a cikin 'yan Najeriyan hakan yayi sanadiyyar mutuwar su

- An ruwaito cewa mutanen suna kan hanyarsu ta zuwa kasar Ehiopia ne daga kasar Brazil

Wani abu marar dadin ji da ya faru da wasu 'yan Najeriya ya sanya mutane da yawa jimami, bayan sunyi kokarin shiga da miyagun kwayoyi daga kasar Brazil zuwa kasar Ethiopia. Mutanen da aka bayyana sunayensu da Chigozie Pascal Aniagbado da kuma Chijioke Chidioka Ogbuefi sun mutu yayin da suka shiga cikin jirgi.

A ruwaito cewa mutanen sun dauki wannan mataki ne na hadiye kwayoyin saboda kada a kama su a filin jirgi, hakan yasa suka hadiye duka kwayoyin da zasu shiga dasu kasar Ethiopia.

Mutanen sun fara shiga wani hali ne yayin da kwayar ta fashe a cikinsu, sun mutu a cikin jirgin kafin ya samu ya sauka duk kuwa da irin kokarin da likitocin cikin jirgin suka yi na ceto rayuwarsu.

KU KARANTA: Mijin Aisha Zakari matar da take tsorata gwamnan Kebbi ta wayar salula ya tona asirin asalin abinda ya faru

Wani wanda yake zaune a kusa da mutanen ya bayyana cewa yaga lokacin da daya daga cikinsu ya fara yin wasu abubuwa wanda bai gane ba, ya ce ya nemi a kawo masa ruwa, abinci, ya ce har mai sai da ya dauka ya fara sha saboda ya rasa yadda zai yi.

Mutumin ya ce marigayin ya bayyana masa cewa kwayar da ya sha din ta dauki lokaci da yawa a cikinsu ne ta fashe, ya ce bayan ya sha man zaitun din kawai sai ya fara karkarwa sai ya fadi.

A cewar shaidar, ya ce likitoci na zuwa suka fara tambayar shi yayi musu bayani, sai suka fara kokarin ceto ransa su, amma ina idan lokaci yayi kira.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel