Daliban makarantar Islamiyya 26 sun mutu a sanadiyyar tashin gobara

Daliban makarantar Islamiyya 26 sun mutu a sanadiyyar tashin gobara

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, wata mummunar gobara ta tashi da tsakar dare a makarantar Islamiyya a Monrovia, babban birnin kasar Liberia, wanda ta yi sanadiyyar mutuwar dalibai 26 da malamansu guda 2.

Rahoton kamfanin dillancin labaru ta AFP ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tace jami’an kashe gobara na kasar Liberia sun shaida ma shugaban kasar, George Weah cewa akalla mutane 28 ne suka mutu a sakamakon gobarar.

KU KARANTA: Rusau a Kaduna: Yan kasuwannin Kaduna sun fara yi ma El-Rufai addu’a

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin shugaban kasa George Weah, Solo Kelgbeh ya bayyana cewa tuni shugaban kasar ya isa makarantar dake yankin Paynesville, a bayan garin Monrovia.

Shugaban al’ummar Fulanin yankin, Amadou Sheriff ya bayyana cewa wutar ta tashi ne a daidai lokacin da daliban ke barci a makarantar Islamiyyar, wanda makarantar kwana ce.

Shi ma shugaban kasa George Weah ya bayyana alhininsa bisa wannan bala’i daya auku, inda ya rubuta a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter cewa:

“Ina taya yan uwa da iyayen yaran nan da suka mutu a garin Paynesville a sakamakon wannan gobara da ta tashi a makarantarsu, alhinin mutuwarsu, hakika kafatanin al’ummar Liberia na cikin halin jimami a yanzu.”

An hangi dandazon iyaye, yan uwa da kuma dangin mamatan sun yi cincirindo a kofar shiga makarantar suna cikin halin jimami da alhini. Da fatan Allah Ya jikan wadanda suka mutu, Amin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel