Yanzu Yanzu: Kotun zabe ta yi watsi da karar da PDP ta shigar kan Gwamna Abubakar Sani Bello a Neja

Yanzu Yanzu: Kotun zabe ta yi watsi da karar da PDP ta shigar kan Gwamna Abubakar Sani Bello a Neja

Kotun zaben gwamna a jihar Neja ta yi watsi da karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta Umar Nasko suka shigar kan Gwamna Abubakar Bello na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Jam’iyyar PDP da dan takararta suna kalubalantar nasarar Bello a zaben gwamna da aka gudanar kwanan nan, cewa gwamnan ya gabatar wa da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da takardun shaidar karatu na bogi.

Kotun zaben karkashin jagorancin John Igboji, yayinda yake watsi da karar yace yana cike da tozarta tsarin kotu saboda wata babbar kotun tarayya ta riga ta saurari karar sannan ta yanke hukunci.

Haka zalika kotun zaben ta riki rashin amincewar wacce ake kara na biyu (APC) akan karar da Umar Nasko da PDP suka shigar kan zargin takardun bogi akan Gwamna Abubakar Bello, kan dalili iri guda.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya koka bayan tsallake rijiya da baya, yace wani malamin addini yayi masa biza na bogi

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa ‘Dan takarar shugaban kasar jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya a zaben 2019, Obadiah Mailafia, ya bayyana yadda APC ta nemi ya dawo cikin tafiyar jam’iyyar saboda a yafe masa zunubansa.

A Ranar Talata, 17 ga Watan Satumban 2019, Obadiah Mailafia yake cewa jam’iyyar APC mai mulki ta yi kokarin janyo sa a jikin ta da nufin za a yafe masa laifin da bai taba aikatawa a Duniya ba.

A cewarsa, Jiga-jigan APC sun yi tunanin ya na harin shigowa jam’iyyar ne bayan zabe. Mailafia ya yi wannan bayani ne lokacin da ya zanta da Menama labarai a Hedikwatar ADC a Garin Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel