Wata sabuwa: Kotu ta haramtawa iyaye dukan 'ya'yansu

Wata sabuwa: Kotu ta haramtawa iyaye dukan 'ya'yansu

- An haramta wa iyaye dukkan 'ya'yansu a kasar Afirka Ta Kudi

- Hakan ya biyo bayan wata hukunci da alkalan babban kotun kasar suka yanke kan wani mahaifi da ya doki dansa

- Kotun ta ce dukan yara keta hakokinsu ne duba da cewa ba su iya kare hansu kuma akwai wasu hanyoyin ladabatarwa da ba su kai duka ila ba

Babban kotun kasar Afirka Ta Kudu a ranar Laraba ta tabbatar da hukuncin da aka yanke na cewa yi wa yara duka a gida ya sabawa dokar kasa ne inda ta ce hakan keta hakkin yara ne.

A wata shar'ar da aka dade ana jiran hukuncin kotun, Kotun na Kasar Afirka Ta Kudi ta goyi bayan wani hukunci da aka yanke a shekarar 2017 inda kotu da daure wani mahaifi da ya doki dansa mai shekaru 13 bayan ya kama shi yana kallon fina-finan batsa.

Wata kungiyar kare hakkin masu addini ta kallubalanci hukuncin inda ta ce ba ta goyon bayan cin zarafin yara amma iyaye suna da ikon su tarbiyantar da 'ya'yansu bisa tafarkin koyarwar addinansu.

DUBA WANNAN: Kotu ta kwace kujerar dan majalisa PDP a jihar Sokoto, ta bayar da umurnin yin zaben raba gardama

Sai dai alkalan guda tara sun cimma matsaya kan cewa ya zama dole a haramta dukkan yara.

Alkalan sun ce "Duba da cewa yara ba su iya kare kansu da kuma tabbatar musu da daraja da kimar da suke da shi a matsayin 'yan adam ya sa dole a haramta dukkan tunda akwai hanyoyin hukunci da ba su kai duka ba."

Kotun ta hana duka a gidajen yari a shekarar 2005 sannan ta haramta duka a makarantu a shekarar 2000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel