Bayan nadin kwamitin tattalin arziki Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa (hotuna)

Bayan nadin kwamitin tattalin arziki Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa (hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Shugaban kasa da ke Abuja, a Laraba,18 ga watan Satumba.

Hakan na zuwa ne bayan Shugaban kasar ya kafa wani kwamiti na musamman da za ta rika ba shi shawara game da harkokin da su ka shafi tattalin arziki.

Wannan shine karo na biyu da Buhari ke ganawa da yan majalisarsa tun bayan kama mulkinsa a karo na biyu.

Ga hotunan taron majalisar:

KU KARANTA KUMA: Yan sandan Neja sun kama mutane 5 kan kisan wani da ake zargi da sace budurwarsa

Idan dai za ku tuna ganawar farko ta majalisar zartarwa ta tarayyar Najeriya wato FEC ta zo ne a daidai lokacin da ake fafatawa a kotu tsakanin Shugaba Buhari da Atiku Abubakar, inda PDP da Atiku ke kalubalantar nasarar Shugaba Buhari a zaben 23 ga watan Fabrairu.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Majalisar zartarwa ta kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma ta roki gwamnatin Najeriya da ta bude iyakokinta da ta rufe.

Kakakin majalisar, Hon. Moustapha Cisse Lo, ya yi wannan kiran ne a taron majalisar zartarwar kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma kashi na biyu da aka yi a Monrovia, Liberia.

Ya kara da cewa, rufe iyakokin ya zama barazana ga yarjejeniyar shiga da ficen da ke tsakanin kasashen. Kuma hakan yazo ne a lokacin da Afirka ke bukatar kokarin cire duk wani shinge tsakanin kasashenta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel