Damuwa a fadar shugaban kasa a kan makomar mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo

Damuwa a fadar shugaban kasa a kan makomar mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo

- Shugaban Muhammadu Buhari ya kwatanta mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da mataimaki mai tsananin biyayya

- Abinda ya faru a daren jiya ya kawo damuwa a zukatan gwamnati da jam'iyya mai mulki ta APC

- Tuni dai Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar da babu wata baraka a fadar shugaban kasar

Makomar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda shugaban kasar ya kwatanta da mataimaki mai biyayya ta sagale a daren jiya Talata.

Farfesa Yemi Osinbajo yana taka rawar gani a gwamnatin nan fiye ma da mataimakin shugaban kasa. Mutum ne mai kaifin basira da ya nakalci dokokin tattalin arzikin mulkin nan.

Amma a ranar Litinin, fadar shugaban kasa ta sanar da maye gurbin kungiyar tattalin arziki (EMT), wacce Osinbajo ke jagoranta, da kungiyar shawara akan tattalin arziki (EAC), wacce Farfesa Doyin Salami ke jagoranta.

Sauran 'yan sabuwar kungiyar sune Dr. Mohammed Sagagi ( mataimakin shugaba), Farfesa Ode Ojowu, Dr Shehu Yahaya, Dr Iyabo Masha, Farfesa Chukwuma Soludo, Bismarck Rewane da Dr Mohammed Adaya Salisu (sakatare).

Mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa akan yada labarai, Femi Adesina, yace kungiyar masu bada shawarar "Zasu dinga bada rahoto kai tsaye ga shugaban kasar".

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ta kwashe gidan shakatawar gwamna, dan majalisa da gidaje 300 a jihar Anambra

Kasa da sa'o'i 24 na samar da sabon kwamitin, damuwa ta samu ga gwamnatin da jam'iyyar APC mai mulki akan zargin shirin canza wasu manyan mataimaka na musamman ga mataimakin shugaban kasan daga fadar shugaban kasan zuwa wasu ma'aikatun da cibiyoyin.

Wannan cigaban ya kara tabbatar da ikirarin cewa akwai masu son ganin sun ragewa mataimakin shugaban kasar karfi ta hanyar karbe wasu cibiyoyi da ke karkashin kulawarsa.

Karin abin tsoron kuwa shine takardar da ake zargi shugaban kasar ya umarci mataimakin nasa da ya dinga neman yarjewar fadar shugaban kasar kafin aiwatar da aiyukan cibiyoyin da ke karkashin ikonsa.

Amma kuma Osinbajo ya musanta cewa akwai baraka a fadar shugaban kasar.

Ya ce cibiyoyin da ke karkashinsa na aiki ne da kundin tsarin mulkin kasa.

Kamar yadda mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande ya ce: "Mun gano cewa akwai wani rahoto da jaridar The Cable ta bada mai ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci mataimakinsa da ya dinga neman amincewarsa kafin zartar da aiyukan cibiyoyin da ke karkashinsa. Wannan rahoton ba gaskiya ba ne."

"Rahoton ya kara da cewa cibiyoyin da me karkashin mataimakin shugaban kasar ba sa bin dokokin kasar. Wannan ba gaskiya bane kuma an fada ne su dasa matsala a fadar shugaban kasar."

"Ciniyoyin da ake magana doka ce ta kafasu kuma mataimakin shugaban kasar na jaddada bin dokar kasa ga kungiyoyin."

Mataimakin shugaban kasar yace bai taba kin bin doka ba.

Ya ja hankalin mutane akan yunkurin kawo matsala a fadar shugaban kasar ballantana tsakaninsa da Shugaban kasar. Ya ce yana da dangantaka da hulda mai kyau tsakaninsa da shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel