Yanzu-yanzu: Matasa sunyi zanga-zanga kan hadarin mota da KASTELEA ta janyo a Kaduna

Yanzu-yanzu: Matasa sunyi zanga-zanga kan hadarin mota da KASTELEA ta janyo a Kaduna

Hankulan al'umma ya tashi a Kaduna yayin da wasu matasa su kayi zanga-zanga kan hadarin motar da aka ce jami'an hukumar kula da ababen hawa da muhalli ta jihar Kaduna (KASTELEA) ne suka yi sanadi a babban titin Nnamdi Azikwe da ke jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa hadarin da ya faru misalin karfe 9 na safe ya janye cikinson motocci sakamakon rufe titi da direbobin tanka su kayi.

Wadanda abin ya faru a gabansu sun ce hadarin ya ritsa ne da wata bas mai daukan mutum 18 da ke dawowa daga tafiya.

Masu zanga-zangar da suka mamaye titin ba su hakura sun bar titin ba duk da cewa shugaban karamar hukumar Kaduna ta Kudu ya ziyarci wurin da abin ya faru ya kuma roke su.

KU KARANTA: Kotu ta kwace kujerar dan majalisa PDP a jihar Sokoto, ta bayar da umurnin yin zaben raba gardama

Daga bisani sai da jami'an tsaro suka iso wurin sannan suka tarwatsa matasan ta hanyar amfani da barkonon tsohuwa.

An gano cewar 'yan kastelea sun bukaci direban motan ya tsaya amma bai tsaya ba hakan yasa jami'in ya yi kokarin tilastawa direban tsayawa ta hanyar murde sitiyarin motar wadda hakan yasa motar ta fada wani rami a gefen titi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa wasu daga cikin fasinjojin motar 18 sun samu rauni kuma an garzaya da su asibiti don yi musu magani.

Wani direba da abin ya faru a gabansa ya ce, "Abinda muke so shine gwamnati ko shugabanin KASTELEA su biya mu asarar da mukayi saboda abinda ya faru abin takaici ne. Adalci muke so a kasar nan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel