Talauci ya kama PDP, za ta rage yawan ma'aikatan hedkwatarta

Talauci ya kama PDP, za ta rage yawan ma'aikatan hedkwatarta

Kwamitin uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sanar da ma'aikatan hedkwatarta dake Abuja da kwalejin PDP cewa za ta rage yawansu.

Uwar jam'iyyar ta nada kwamiti kan aiwatar da wannan sallama amma har yanzu kwamitin bata kammala tattaunawa a kai ba.

An samu labarin cewa zancen rage ma'aikata ne babban dalilin zaman tattaunawa da ma'aikatan hedkwatar PDP da uwar jam'iyyar.

Hakazalika, jam'iyyar na shirin biyan wadanda doka ya wajabta biyansu gratuti kamar yadda dokar kafa jam'iyyar ya tanada kuma shugaban jam'iyyar, Uche Secondus, ya sanya hannu.

A cewar takardar yarjejeniya da shugaban jin dadin ma'aikatan jam'iyyar, Innocent Nwankwo, ya sanya hannu, kudin da ake biyan ma'aikatan a kowani wata N15m ne kuma ma'aikatansu 96 ne.

Nwankwo ya ce rage yawan ma'aikatan ya zama wajibi saboda kudin ya yi yawa jam'iyyar.

Ya kara da cewa ba wai talauci ne ya kama su ba saboda suna da gwamnoni 16, Sanatoci 44, yan majalisan wakilai 131, yan majalisun jihohi 390.

A wani labarin daban, Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ce gwamnatin Najeriya ba za ta kai karan kasar Afirka ta kudu majalisar dinkin duniya ba kan cin zarafin yan Najeriya a taron gangamin da zai gudana a wannan watan a birnin New York, Amurka.

Ministan ya kara da cewa ana tattaunawar diflomasiyya kan ganin yadda za'a biya yan Najeriyan da abin ya sha wasu kudade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel