Magu ya fadawa tsohon ministan shari'a ya gurfanar da kansa gaban kotu

Magu ya fadawa tsohon ministan shari'a ya gurfanar da kansa gaban kotu

- Mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa ya nuna damuwarsa akan zarginsa da tsohon ministan shari'a yake masa

- Magu ya kwatanta zargin da tsohon ministan shari'a ya rubuta a littafinsa da hanyar samun kasuwa

- Shugaban hukumar EFCC ya bukaci tsohon ministan shari'a da ya gurfana gaban kotu don fuskantar shari'a

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu, ya nuna damuwarsa akan zargin da tsohon ministan shari'a, Mohammed Adoke, ya yi ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Tsohon ministan shari'ar ya ce mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo na amfani da hukumar yaki da rashawa ta EFCC don muzguna masa.

Magu ya kwatanta zargin da ke kunshe a cikin littafin da Adoke ya wallafa da wani salo na samun kasuwa.

A cikin littafinsa mai suna "Burden of Service: Reminiscences of Nigeria's former Attorney General," wanda tsohon ministan shari'a ya rubuta, ya zargi Magu, Osinbajo da tsohon shugaban majalisar dattawa, Alli Ndume, da hada kai don bata shi, har ta kai ga yana tunanin kashe kansa.

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ta kwashe gidan shakatawar gwamna, dan majalisa da gidaje 300 a jihar Anambra

Amma a ranar Talata, shugaban EFCC ta bakin mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujare, yace Adoke ya mika kansa don shari'a.

Yace, "Mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, babu lokacin da mataimakin shugaban kasar ya tattauna da shi, ya bada shawara ko ya umarcesa akan wani abu da ya shafi Adoke. Ba abu ne mai kyau ba da zaka zargi wani da aikata wannan abu ba."

"Akwai dama karar cin hanci da hukumar ta binciko akan Adoke, Dan Etete da sauransu da ke gaban babban kotun tarayya da ke Abuja."

"An kasa gurfanar dasu ne gaban kuliya sakamakon Adoke da sauran wadanda ake zargin har yanzu sun ki bayyana gaban kotun."

"Bayan cika burinsa na nishadantar da mutane da tatsuniyoyinsa, zai fi cancanta da ya gurfanar da kansa gaban shari'a," inji hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel