Ba zamu kai karan kasar Afirka ta kudu majalisar dinkin duniya ba - FG

Ba zamu kai karan kasar Afirka ta kudu majalisar dinkin duniya ba - FG

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ce gwamnatin Najeriya ba za ta kai karan kasar Afirka ta kudu majalisar dinkin duniya ba kan cin zarafin yan Najeriya a taron gangamin da zai gudana a wannan watan a birnin New York, Amurka.

Ministan ya kara da cewa ana tattaunawar diflomasiyya kan ganin yadda za'a biya yan Najeriyan da abin ya sha wasu kudade.

Da aka tambayesa shin za suyi magana kan harin kin jinin bakin fatan da aka kaiwa yan Najeriya a kasar Afrika ta kudu, yace:

"Bamu kai wannan wurin ba. Kuma ban tunanin muna bukatar hakan. Ina tunanin abune da zamu iya tattaunawa tsakaninmu."

A ranar Litinin, shugaba Muhammadu Buhari ya amince da hakurin shugaban kasar Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, kan hare-haren da aka kaiwa yan Najeriya a kasarsa.

Shugaba Buhari, wanda ya siffanta wannan hare-hare a matsayin abin takaici ya ce duk da hakan, za'a cigaba da karfafa alaka tsakanin kasashen guda biyu.

Buhari ya tunawa wakilan shugaban kasan irin namijin gudunmuwar da Najeriya ta baiwa kasar Afirka ta kudu saboda yawancin matasan kasar sun jahilci tarihi.

Shugaba Buhari ya gana da wakilan shugaban kasar Afrika ta kudu na musamman Dr. K. Mbatta da Jeff Radebe a birnin tarayya Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel